Irmiya 15:6 - Littafi Mai Tsarki6 Ni Ubangiji na ce, kun ƙi ni, kuna ta komawa da baya, Don haka na nuna ikona gāba da ku, na hallaka ku, Na gaji da jin tausayinku! အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20206 Kin ƙi ni,” in ji Ubangiji. “Ki ci gaba da ja da baya. Ta haka zan ɗibiya hannuwana a kanki in hallaka ki; ba zan ƙara nuna miki jinƙai ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Don haka ina cike da fushin Ubangiji Na gaji da kannewa. Ubangiji ya ce, “Zan kwararo fushi kan yara da suke a titi. Da kuma kan tattaruwar samari. Za a ɗauke mata da miji duka biyu, Da tsofaffi, da waɗanda suka tsufa tukub-tukub. Za a ba waɗansu gidajensu, da gonakinsu, da matansu, Gama zan nuna ikona in hukunta mazaunan ƙasar.