Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 15:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Zan maishe ka garun tagulla saboda waɗannan mutane, Za su yi yaƙi da kai, amma ba za su yi nasara a kanka ba, Gama ina tare da kai don in cece ka, in kuɓutar da kai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Zan mai da kai katanga ga wannan mutane, katanga mai ƙarfi na tagulla; za su yi yaƙi da kai amma ba za su yi nasara a kanka ba, gama ina tare da kai don in kuɓutar in kuma cece ka,” in ji Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 15:20
27 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kamar yadda lu'ulu'u ya fi ƙanƙarar dutse ƙarfi, haka nan na sa goshinka ya zama. Kada ka ji tsoronsu, ko kuwa ka karai saboda irin kallon da za su yi maka, gama su 'yan tawaye ne.”


Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare da kai, Zan kiyaye ka. Ni Ubangiji na faɗa.”


Kada ka ji tsoro, ina tare da kai, Ni ne Allahnka, kada ka bar kome ya firgita ka. Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka, Zan kiyaye ka, in cece ka.


Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu, Allah na Yakubu shi ne mafakarmu!


Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu, Allah na Yakubu shi ne mafakarmu!


Ubangiji yă kasance a zuciyarka. alheri yă tabbata a gare ku.


Ubangiji ya ce wa Irmiya, “Na maishe ka mai aunawa da mai jarraba mutanena Domin ka sani, ka auna al'amuransu,


Yanzu fa, Ubangiji kansa zai ba ku alama. Wata budurwa wadda take da ciki, za ta haifi ɗa, za a raɗa masa suna Immanuwel.


Kaitona, ya mahaifiyata, da kika haife ni, mai jayayya mai gardama da kowa cikin dukan ƙasar! Ban ba da rance ba, ba kuma wanda ya ba ni rance, duk da haka dukansu suna zagina.


Sa'an nan Irmiya ya ce, “Ya Ubangiji, ka sani. Kai ne, ka ziyarce ni, Ka kuma sāka wa waɗanda suke tsananta mini. Ka sani saboda kai nake shan zargi.


Irmiya kuwa ya yi zamansa a gidan waƙafi har ranar da aka ci Urushalima da yaƙi.


Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya yi wa Nebuzaradan shugaban matsara umarni a kan Irmiya ya ce,


Kada ku ji tsoron Sarkin Babila, shi wanda kuke jin tsoronsa. Kada ku ji tsoronsa,’ in ji Ubangiji, ‘gama ina tare da ku, zan cece ku, in kuɓutar da ku daga hannunsa.


Idan haka ne, Allahnmu wanda muke bauta wa, yana da iko ya cece mu daga tanderun gagarumar wuta, zai kuwa kuɓutar da mu daga hannunka, ya sarki.


Ubangiji yakan ceci adalai, Ya kiyaye su a lokatan wahala.


Ga shi, na sa fuskarka da goshinka su zama da tauri kamar nasu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ