Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 14:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Ya kai, wanda kake begen Isra'ila, Mai Cetonta a lokacin wahala, Ƙaƙa ka zama kamar baƙo a ƙasar? Kamar matafiyi wanda ya kafa alfarwarsa a gefen hanya don ya kwana, ya wuce?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Ya kai, Sa Zuciyar Isra’ila, Mai Cetonsa a lokutan wahala, me ya sa kake yi kamar baƙo a ƙasar, kamar matafiyi wanda yake shirya wuri don yă kwana gari ya waye ya wuce?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 14:8
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya Ubangiji, begen Isra'ila, Duk waɗanda suka rabu da kai, za su sha kunya. Waɗanda suka ba ka baya a duniya za a rubuta su Domin sun rabu da Ubangiji, maɓuɓɓugar ruwan rai.


Duk waɗanda suka same su, sun cinye su. Maƙiyansu suka ce, ‘Ba mu yi laifi ba,’ Gama sun yi wa Ubangiji laifi, wanda yake tushen gaskiya, Ubangiji wanda kakanninsu suka dogara gare shi.


Gama ni ne Ubangiji Allahnku, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, wanda ya cece ku. Zan ba da Masar, da Habasha, da Seba Ga Sairus domin fansarku.


Ku yi kira gare ni sa'ad da wahala ta zo, Zan cece ku, Ku kuwa za ku yabe ni.”


Ubangiji yana magana da ƙarfi daga Sihiyona, Yana tsawa daga Urushalima, Sammai da duniya sun girgiza. Amma Ubangiji shi ne mafakar jama'arsa, Shi ne kagarar mutanen Isra'ila.


Ku zo ku gabatar da matsalarku a ɗakin shari'a, Bari waɗanda aka kai ƙara su yi shawara da juna. Wane ne ya faɗi abin da zai faru, Ya kuma yi annabci tuntuni? Ashe, ba ni ba ne, Ubangiji, Allah wanda ya ceci mutanensa? Ba wani Allah sai ni.


“Ni kaɗai ne Ubangiji, Ni kaɗai ne wanda yake da ikon yin ceto.


Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu bisa ga umarnin Allah Mai Cetonmu, da kuma na Almasihu Yesu abin begenmu,


Shi ya sa na nema in gana da ku, tun da yake dai saboda sa zuciyar nan da Isra'ila take yi ne nake ɗaure da sarƙan nan.”


Allah na Isra'ila, wanda ya ceci mutanensa, Shi ne yakan ɓoye kansa.


Ko lokacin da nake tsakiyar wahala, Za ka kiyaye ni lafiya, Ka yi gāba da abokan gābana, waɗanda suka husata, Za ka kuwa cece ni da ikonka.


Sa'ad da suka kira gare ni, zan amsa musu, Zan kasance tare da su sa'ad da suke shan wahala, Zan cece su in girmama su.


Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, Kullum a shirye yake yă yi taimako a lokacin wahala.


Ubangiji mafaka ne ga waɗanda ake zalunta, Wurin ɓuya a lokatan wahala.


Ya Ubangiji, me ya sa kake can nesa? Me ya sa ka ɓoye kanka a lokacin wahala?


Da dattijon ya duba ya ga matafiyin a dandalin birnin, ya ce masa, “Ina za ka? Daga ina kuma ka fito?”


Ya Ubangiji, a gare ka nake sa zuciya, Tun ina yaro, nake dogara gare ka.


Ubangiji ya ce, “Su mutanena ne, ba za su ruɗe ni ba.” Saboda haka kuwa ya cece su


Kaito, gama wannan babbar rana ce, Ba kuma kamarta, Lokaci ne na wahala ga Yakubu, Duk da haka za a cece shi daga cikinta.”


Ku koma mafakarku, ku ɗaurarru masu sa zuciya. Gama yanzu zan sāka muku har ninki biyu.


Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, Ko da duniya za ta girgiza, Duwatsu kuma su fāɗa cikin zurfafan teku,


Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai. Muna sa zuciyarmu gare ka. Ka dinga kiyaye mu yau da gobe, ka kuma cece mu a lokatan wahala.


“Ya Ubangiji, ƙarfina da kagarata, Mafakata a ranar wahala, A gare ka al'ummai za su zo, Daga ƙurewar duniya, su ce, ‘Kakanninmu ba su gāji kome ba, sai ƙarya, Da abubuwan banza marasa amfani.’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ