Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 14:17 - Littafi Mai Tsarki

17 “Irmiya, ka faɗa wa mutanen baƙin ciki da ya same ka, Ka ce, ‘Bari idanuna su yi ta zub da hawaye dare da rana, Kada su daina, saboda an buge budurwa, 'yar jama'ata, An yi mata babban rauni da dūka mai tsanani.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 “Ka yi musu wannan magana, “ ‘Bari idanuna su yi ta zub da hawaye dare da rana kada su daina; saboda ’yata budurwa, mutanena, sun sha wahalar babban rauni, an yi musu bugu mai ragargazawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 14:17
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Raunin da aka yi wa jama'ata, Ya yi wa zuciyata rauni. Ina makoki, tsoro kuma ya kama ni ƙwarai.


Me zan ce miki? Da me zan kwatanta ki, ya Urushalima? Da me zan misalta wahalarki Don in ta'azantar da ke, ya Sihiyona? Masifar da ta same ki tana da fāɗi kamar teku, Wa zai iya warkar da ke?


Amma idan ba za ku ji ba, Raina zai yi kuka a ɓoye saboda girmankanku, Idanuna za su yi kuka ƙwarai, za su zub da hawaye, Domin an kai garken Ubangiji zuwa bauta.


Da ma kaina ruwa ne kundum, Idanuna kuma maɓuɓɓuga ne, Da sai in yi ta kuka dare da rana, Saboda an kashe jama'ata!


Domin haka zan buge ku da ciwo, In maishe ku kufai saboda zunubanka.


Ya Sihiyona, ki yi kuka ga Ubangiji, Bari hawayenki su gudana dare da rana kamar ruwan rafi, Kada ki huta, kada kuma idanunki su huta!


Tawa ta ƙare, saboda raunin da aka yi mini. Raunina mai tsanani ne, Amma na ce, lalle wannan azaba ce, Tilas in daure da ita.


Ubangiji ya ce, “Birnin Urushalima yana yi maka dariya, kai Sennakerib, yana kuma yi maka ba'a.


Kada ka ƙara hukunta ni! Na kusa mutuwa saboda bugun da kake yi mini!


Isra'ila ta fāɗi, Ba kuwa za ta ƙara tashi ba. Tana fa kwance a ƙasa, Ba wanda zai tashe ta.


Hawayena suna malalowa kamar kogi, Saboda jama'a ba su biyayya da shari'arka ba.


Baƙin cikina ya fi ƙarfin warkewa, Zuciyata ta ɓaci ƙwarai!


Ubangiji ya ce, “Birnin Urushalima ya yi maka dariya, kai Sennakerib, yana yi maka ba'a.


Jama'a suka ce, “Su gaggauta, su ta da murya, Su yi mana kuka da ƙarfi, Har idanunmu su cika da hawaye, Giranmu kuma su jiƙe sharaf.


“Domin haka ni Ubangiji na ce, ‘Ka tambayi sauran al'umma. Wa ya taɓa jin irin wannan? Budurwa Isra'ila, ta yi mugun abu ƙwarai!


Idanuna sun dushe saboda kuka, Raina yana cikin damuwa. Zuciyata ta karai saboda halakar mutanena, Gama 'yan yara da masu shan mama Sun suma a titunan birnin.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ