Urushalima ta yi zunubi ƙwarai da gaske, Saboda haka ta ƙazantu, Dukan waɗanda suka girmama ta sun raina ta Domin sun ga tsiraicinta, Ita kanta ma tana nishi, ta ba da baya.
domin haka zan tattara miki daga kowane waje dukan kwartayenki, waɗanda kika yi nishaɗi da su, wato dukan waɗanda kika ƙaunace su, da waɗanda kika ƙi. Zan sa su yi gāba da ke. Zan buɗe musu tsiraicinki don su gani.
Amma na tsiraita Isuwa sarai, Na buɗe wuraren ɓuyarsa, Har bai iya ɓoye kansa ba, An hallakar da mutanen Isuwa Tare da 'yan'uwansa da maƙwabtansa, Ba wanda ya ragu.
Zan ɓata inabinta da itatuwan ɓaure Waɗanda take cewa, ‘Waɗannan su ne hakkina Wanda samarina suka ba ni.’ Zan sa su zama kurmi, Namomin jeji su cinye su.