Don haka za su zama kamar ƙāsashin da akan yi da safe, Ko kuwa kamar raɓa mai kakkaɓewa da wuri. Za su zama kamar ƙaiƙayi wanda ake shiƙarsa cikin iska a masussuka, Ko kuwa kamar hayaƙin da yake fita ta bututu.
Sai ka ƙone kashi ɗaya da wuta a tsakiyar birnin sa'ad da kwanakin kewaye birnin da yaƙi suka cika. Ka kuma ɗauki sulusi ɗaya ka yanyanka da takobi kewaye da birnin. Sulusi ɗayan kuwa za ka watsar ya bi iska. Ni kuwa zan zare takobi a kansu.
Za a kashe waɗansu da kaifin takobi, a kuma kakkama waɗansu a kai su bauta zuwa ƙasashen al'ummai duka. Al'ummai kuma za su tattake Urushalima, har ya zuwa cikar zamaninsu.”
Za ku watsa su sama cikin iska, Iska za ta hure su, ta tafi da su, Hadiri kuma zai warwatsar da su. Amma za ku yi murna, gama ni ne Allahnku, Za ku yabe ni, Allah Mai Tsarki na Isra'ila.
Al'ummai sun ci gaba kamar sukuwar raƙuman ruwa, amma Allah ya tsauta musu suka kuwa janye, aka kora su kamar ƙura a gefen dutse, kamar kuma tattaka a cikin guguwa.
“Ubangiji zai warwatsa ku cikin dukan al'ummai daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Can za ku bauta wa gumakan itace da na dutse waɗanda ku da kakanninku ba ku san su ba.
“Ubangiji ya yi watsi da majiya ƙarfina, Ya kirawo taron jama'a a kaina Don su murƙushe samarina. Ya kuma tattake Urushalima, zaɓaɓɓiyarsa, Kamar 'ya'yan inabi a wurin matsewa.