Irmiya 13:19 - Littafi Mai Tsarki19 An kulle biranen Negeb, Ba wanda zai buɗe su, Yahuza duka an kai ta zaman dole, Dukanta an kai ta zaman dole. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202019 Za a kulle biranen da suke a Negeb, kuma babu wanda zai buɗe su. Za a kwashe dukan Yahuda zuwa zaman bauta, za a kwashe su tas. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Za a sayi gonaki da kuɗi, a sa hannu a kan sharuɗa, a hatimce su a gaban shaidu, a ƙasar Biliyaminu da wuraren da suke kewaye da Urushalima, da cikin garuruwan Yahuza, da na garuruwan ƙasar tudu, da a garuruwan kwaruruka, da a garuruwan Negeb, gama zan komar wa mutane da wadatarsu a ƙasarsu, ni Ubangiji na faɗa.”
Bayan da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kama Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, daga Urushalima, ya kai shi bautar talala a Babila, tare da sarakunan Yahuza, da gwanayen sana'a, da maƙera, dukansu, ya kawo su Babila. Sai Ubangiji ya nuna mini wannan wahayi. Na ga kwando biyu na ɓaure, an ajiye su a gaban Haikalin Ubangiji.