Ku dattawa, ku kasa kunne, Bari kowa da kowa da yake cikin Yahuza, ya kasa kunne. Wani abu mai kamar wannan ya taɓa faruwa a lokacinku, Ko a lokacin kakanninku?
Ku tabbata dai, idan kuka kashe ni, za ku jawo hakkin jinin marar laifi a kanku da a kan wannan birni da mazauna a cikinsa, gama a gaskiya Ubangiji ne ya aiko ni wurinku domin in faɗa muku dukan maganan nan a kunnuwanku.”