Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 13:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Gama kamar yadda abin ɗamara yakan kame tam a gindin mutum, haka na sa dukan mutanen Isra'ila da dukan mutanen Yahuza su manne mini domin su zama jama'a, da suna, da yabo, da daraja a gare ni, amma sun ƙi ji.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Gama kamar yadda abin ɗamara kan kame gindin mutum tam, haka zan daure dukan gidan Isra’ila da dukan gidan Yahuda gare ni,’ in ji Ubangiji, ‘domin su zama jama’a, da suna, da yabo, da daraja a gare ni, amma sun ƙi ji.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 13:11
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sunan wannan birni zai zama mini abin murna, da abin yabo, da darajantawa ga dukan al'umman duniya waɗanda za su ji dukan alherin da na yi dominsu, za su ji tsoro su yi rawar jiki saboda dukan alheri da dukan wadata da na tanada musu.”


Su ne mutanen da na yi domin kaina, Za su raira yabbaina!”


“Amma jama'ata ba su kasa kunne gare ni ba. Isra'ila ta ƙi yi mini biyayya.


Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.


Ka aikata alamu da al'ajabai a ƙasar Masar. Har wa yau kuma kana aikata su a Isra'ila da kuma cikin dukan al'ummai, ka yi wa kanka suna kamar yadda yake a yau.


Wannan muguwar jama'a, wadda ta ƙi jin maganata, wadda ta taurare, ta bi son zuciyarta, ta kuma bi gumaka ta bauta musu, ta yi musu sujada, za ta zama kamar abin ɗamaran nan, wanda ba shi da sauran amfani.


Duk da haka ba su saurare ni ba, ba su kula su ji ba, sai suka taurare zukatansu suka aikata mugun abu fiye da na kakanninsu.


Na sa muku matsara cewa, in kun ji an busa ƙaho ku kula! Amma suka ce, ‘Ba za mu kula ba.’


Za a ce da ku, “Tsattsarkar Jama'ar Allah,” “Jama'ar da Ubangiji ya Fansa!” Za a kira Urushalima, “Birnin da Allah yake Ƙauna,” “Birnin da Allah bai Yashe shi Ba.”


Bai yi wa sauran al'umma wannan ba, Domin ba su san dokokinsa ba. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!


Ya zaɓar wa kansa Yakubu, Jama'ar Isra'ila kuwa tasa ce.


Yau kuma Ubangiji ya shaida, cewa ku ne jama'arsa ta musamman, kamar yadda ya alkawarta muku. Ku kuwa za ku kiyaye dukan umarnansa.


“Gama babu wata babbar al'umma wadda allahnta yake kusa da ita kamar yadda Ubangiji Allahnmu yake kusa da mu sa'ad da muka kira gare shi.


‘Ko da ƙurar garinku da ta ɗafe a jikin ƙafafunmu ma, mun karkaɗe muku. Amma duk da haka ku sani Mulkin Allah ya kusato.’


Yanzu kuwa saboda kun aikata waɗannan al'amura, sa'ad da na yi ta yi muku magana, amma ba ku kasa kunne ba, sa'ad da na kira ku, ba ku amsa ba,


Amma na umarce su su yi biyayya da maganata, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena, su bi dukan al'amuran da na umarce su, domin lafiyarsu, don su zama lafiya.


Amma ba su yi biyayya ba, ba su kuma kula ba. Sai suka bi shawarar kansu da ta tattaurar muguwar zuciyarsu. Suka koma baya maimakon su yi gaba.


Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, ya ce, “Tafi ka sayo lilin na yin ɗamara, ka sha ɗamara da shi kada kuwa ka tsoma shi a ruwa.”


“Sai ka faɗa musu wannan magana cewa, ‘Ni Ubangiji Allah na Isra'ila na ce, a cika kowane tulu da ruwan inabi.’ Su kuwa za su ce maka, sun sani sarai za a cika kowane tulu da ruwan inabi.


Jama'ar Isra'ila, ku kasa kunne ga wannan saƙo da Ubangiji ya aiko muku, ya ce, “Na fitar da iyalanku duka daga Masar.


Shi kuwa zai ɗaukaka ku ku zama abin yabo, masu suna, masu daraja, fiye da dukan al'umman da ya yi. Za ku zama jama'a tsattsarka ta Ubangiji Allahnku kamar yadda ya faɗa.”


“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, ‘Ga shi, ina aukar wa wannan birni da dukan garuruwansa dukan masifu da na ambata a kansa, domin sun taurare zukatansu, sun ƙi jin maganata.’ ”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ