Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 13:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Wannan muguwar jama'a, wadda ta ƙi jin maganata, wadda ta taurare, ta bi son zuciyarta, ta kuma bi gumaka ta bauta musu, ta yi musu sujada, za ta zama kamar abin ɗamaran nan, wanda ba shi da sauran amfani.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Waɗannan mugayen mutane, waɗanda suka ƙi saurari maganata, waɗanda suka biye wa taurin zuciyarsu suka bi waɗansu alloli don su bauta su kuma yi musu sujada, za su zama kamar wannan abin ɗamara gaba ɗaya marasa amfani!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 13:10
32 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku kuma kun yi laifi fiye da na kakanninku. Kowannenku kuwa ya bi tattauran mugun nufin zuciyarsa, yana ƙin kasa kunne gare ni.


Amma suka taurare, suka biye wa zuciyarsu, suka bi Ba'al, kamar yadda kakanninsu suka koya musu.


Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe mutanen nan za su raina ni? Har yaushe za su ƙi gaskata ni, ko da yake na aikata alamu a tsakiyarsu?


“Ku kangararru, masu ɓatan basira, masu kunnen ƙashi, kullum kuna yi wa Ruhu Mai Tsarki tsayayya. Yadda kakanninku suka yi, haka ku ma kuke yi.


Sai na tafi Yufiretis, na haƙa na ɗauko abin ɗamara daga wurin da na ɓoye shi. Amma abin ɗamara ya lalace, ba shi da sauran amfani.


In lokacin nan ya yi, za a kira Urushalima gadon sarautar Ubangiji, dukan sauran a'umma za su taru a Urushalima da sunana. Ba za su ƙara bin tattaurar zuciyarsu mai mugunta ba.


Ku kula fa, kada ku ƙi mai maganar nan. Domin in waɗanda suka ƙi jin mai yi musu gargaɗi a duniya ba su tsira ba, to, ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi jin wannan da yake yi mana gargaɗi ma daga Sama?


za su mutu da muguwar cuta. Ba za a yi makoki dominsu ba, ba kuwa za a binne su ba. Za su zama juji. Takobi da yunwa za su kashe su, gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namomin jeji.”


Ubangiji ya sanasshe ni, Na kuwa sani, Sa'an nan ya nuna mini mugayen ayyukansu.


Me ya sa, mutanen nan na Urushalima suke ratsewa, suke komawa baya kullayaumin? Sun riƙe ƙarya kan-kan Sun ƙi komowa.


Amma mutanen nan suna da taurin zuciya, masu halin tayarwa ne, Sun rabu da ni, sun yi tafiyarsu.


Maimakon su riƙa ƙanshin turare, za su yi wari, a maimakon abin ɗamara, za su yi ɗamara da igiyoyi masu kaushi, a maimakon su kasance da kyakkyawan gashi, za su zama masu sanƙo, a maimakon tufafi masu kyau, za su sa tsummoki, kyansu zai zama abin kunya!


Ya saurayi! Ka yi murna a lokacin ƙuruciyarka, ka bar zuciyarka ta yi farin ciki a kwanakin samartakarka. Ka bi nufin zuciyarka da sha'awar idanunka. Amma ka sani fa, a cikin al'amuran nan duka Allah zai shara'anta ka.


Kada su zama kamar kakanninsu, Jama'ar 'yan tawaye marasa biyayya. Ba su taɓa dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya ba, Ba su kuwa yi masa aminci ba.


idan ba ku tsananta wa baƙo, ko maraya, ko gwauruwa, wato matar da mijinta ya rasu, idan ba ku zubar da jinin marar laifi a wannan wuri ba, idan kuma ba ku bi abin da zai cuce ku ba, wato gumaka,


Suna ƙara zalunci a kan zalunci, Yaudara a kan yaudara, Sun ƙi sanina,” in ji Ubangiji.


Sun koma a kan laifofin kakanninsu, waɗanda suka ƙi jin maganata, suka bi gumakansu don su bauta musu, jama'ar Isra'ila da na Yahuza sun ta da alkawarina wanda na yi da kakanninsu.


Haka Ubangiji ya ce, ‘Ga shi, zan maishe ka abin tsoro ga kai kanka, da dukan abokanka. Abokan gābansu za su kashe su da takobi a kan idonka. Zan ba da dukan Yahuza a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai kwashe waɗansu ya kai bautar talala a Babila, ya kuma kashe waɗansu da takobi.


Ubangiji ya yi muku magana a lokacin wadatarku. Amma kun ce, “Ba za mu kasa kunne ba!” Wannan shi ne halinku tun kuna samari, Don ba ku yi biyayya da murya Ubangiji ba.


Suna ta faɗa wa waɗanda suke raina maganar Ubangiji cewa, ‘Za ku zauna lafiya!’ Ga kowane mai bin nufin tattaurar zuciyarsa, ‘Ba masifar da za ta same ka.’ ”


Na yi ta aiko muku da bayina annabawa, ina cewa, kowa ya bar muguwar hanyarsa, ya gyara ayyukansa, kada ya bauta wa gumaka. Ta haka za ku zauna a ƙasa wadda na ba ku, ku da kakanninku, amma ba ku kasa kunne, ku ji ni ba.


Amma ba su kasa kunne ba, ba su kuwa ji ba, da za su juyo daga mugayen ayyukansu na miƙa wa gumaka hadayu.


“Ba za mu kasa kunne ga jawabin da kake yi mana da sunan Ubangiji ba!


Yanzu kuwa saboda kun aikata waɗannan al'amura, sa'ad da na yi ta yi muku magana, amma ba ku kasa kunne ba, sa'ad da na kira ku, ba ku amsa ba,


Sai Ubangiji ya ce, “Saboda sun bar dokata wadda na sa a gabansu, ba su yi biyayya da maganata ko su yi aiki da ita ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ