Irmiya 12:10 - Littafi Mai Tsarki10 Makiyaya da yawa sun lalatar da gonar inabina. Sun tattake nawa rabo, Sun mai da nawa kyakkyawan rabo kufai da hamada. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 Makiyaya masu yawa za su lalace gonar inabina su tattake gonata; za su mai da gonata mai kyau kango marar amfani. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai na ji wani mai tsarki yana magana, wani kuma mai tsarki ya tambayi wancan mai tsarki da ya yi magana, ya ce, “Sai yaushe za a tsai da abubuwan da suke a wahayin nan, wato hana yin hadayar ƙonawa ta yau da kullum, da zunubin da yake lalatarwa, da ba da wuri mai tsarki ga rundunar mutane don a tattake?”