Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 11:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Ba wanda zai ragu daga cikin mutanen Anatot, gama zan kawo wa mutanen Anatot masifa, a shekarar hukuncinsu.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Babu raguwar da za a bar musu, domin zan kawo masifa a kan mutanen Anatot a shekarar hukuncinsu.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 11:23
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Saboda haka hanyarsu za ta zama da santsi da duhu, Inda za a runtume su, su fāɗi. Gama zai kawo musu masifa a shekarar da za su sha hukuncinsu.” Ubangiji ya faɗa.


su fyaɗa ku a ƙasa, ku mutanen birni duka, ba kuma za su bar wani dutse a kan ɗan'uwansa ba a birninku, don ba ku fahimci lokacin da ake sauko muku da alheri ba.”


Mutumin kirkinsu kamar ƙaya yake, Mai gaskiyarsu kuwa kamar shingen ƙaya yake. Ranar da kuka sa mai tsaro, A ran nan za a aukar muku da hukunci. Yanzu ruɗewarku ta zo,


Ranar hukunci ta zo, ranar ramako ta iso, Isra'ila za ta sani! An ce annabi wawa ne, Mutumin da yake da ruhu kuwa mahaukaci ne, Saboda yawan muguntarku da ƙiyayyarku.


Ku kashe dukan bijimanta, a kai su mayanka! Kaitonsu, gama kwanansu ya ƙare, Lokacin hukuncinsu ya yi.


Wanda ya guje wa tsoro, Zai fāɗa a rami, Wanda kuma ya fito daga cikin rami, Tarko zai kama shi. Gama na sa wa Mowab lokacin da zan hukunta ta, Ni Ubangiji na faɗa.


Sojojin ijararta kamar 'yan maruƙa ne, masu yawan kitse, Sun ba da baya, sun gudu, ba su tsaya ba, Domin ranar masifarsu ta zo, Lokacin halakarsu ya yi.


Ga shi, ina lura da su, ba domin alheri ba, amma domin in aukar musu da masifa. Takobi da yunwa za su hallaka dukan mutanen Yahuza waɗanda suke a ƙasar Masar.


Amma ina kama da lafiyayyen ɗan rago, Wanda aka ja zuwa mayanka, Ashe, ni suke ƙulla wa munafuncin! Ni kuwa ban sani ba, da suke cewa, “Bari mu lalatar da itacen duk da 'ya'yansa. Bari mu datse shi daga ƙasar masu rai, Har da ba za a ƙara tunawa da sunansa ba.”


Ko sun ji kunya Sa'ad da suka aikata ayyuka masu banƙyama? A'a, ba su ji kunya ba ko kaɗan, Fuskarsu ko gezau ba ta yi ba. Domin haka za su faɗi tare da fāɗaɗɗu, Sa'ad da na hukunta su, za a ci su da yaƙi. Ni Ubangiji na faɗa.


Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Za a kalace ringin Isra'ila sarai, kamar yadda ake wa inabi, Ka miƙa hannunka a kan rassanta kamar mai tsinkar 'ya'yan inabi.”


“Ba zan hukunta su saboda waɗannan abubuwa ba? Ba zan ɗaukar wa kaina fansa a kan al'umma irin wannan ba?


Ba zan hore su saboda waɗannan abubuwa ba? Ni Ubangiji na ce, ba zan ɗauka wa kaina fansa a kan wannan al'umma ba?


Jama'ar Yakubu za ta zama kamar wuta, Jama'ar Yusufu kuwa kamar harshen wuta, Jama'ar Isuwa za ta zama kamar tattaka. Za su ƙone ta, su ci ta, ba wanda zai tsira. Ni Ubangiji na faɗa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ