Irmiya 11:17 - Littafi Mai Tsarki17 Ubangiji Mai Runduna, wanda ya dasa ku, ya hurta masifar da za ta same ku saboda muguntar da mutanen Isra'ila da na Yahuza suka yi, suka tsokane ni in yi fushi saboda suna ƙona wa Ba'al turare. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202017 Ubangiji Maɗaukaki, wanda ya dasa ki, ya furta miki masifa, domin gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda sun aikata mugunta suka kuma tsokane ni in yi fushi ta wurin ƙona wa Ba’al turare. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Zan nuna wa jama'ata Isra'ila wuri na kansu inda zan kafa su su zauna. Ba wanda zai sāke damunsu. Mugayen mutane kuma ba za su ƙara wahalshe su kamar dā ba, tun lokacin da na naɗa wa jama'ata Isra'ila mahukunta. Zan hutar da kai daga fitinar abokan gābanka duka. Banda wannan kuma ina shaida maka, cewa, zan sa gidanka ya kahu.