Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 10:9 - Littafi Mai Tsarki

9 An kawo fallayen azurfa daga Tarshish, Da zinariya kuma daga Ufaz, Aikin gwanaye da maƙeran zinariya. Tufafinsu na mulufi ne da shunayya, duka aikin gwanaye.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 An kawo ƙeraren azurfa daga Tarshish zinariya kuma daga Ufaz. Abin da gwani da maƙerin zinariya suka yi sa’an nan aka yi masa ado da mulufi da shunayya dukan aikin gwanaye.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 10:9
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma nasu alloli na azurfa da zinariya ne, Da hannu aka siffata su.


Da na ɗaga kaina sai na ga wani sāye da rigar lilin, ya ɗaura ɗamara ta zinariya tsantsa.


Shi ba kamar gunki yake ba, wanda mutane suka yi, Maƙera kuma suka dalaye da zinariya, Suka sa shi cikin abin da suka yi da azurfa.


Gama sarki yana da rundunar jiragen ruwa a tekun Tarshish tare da na Hiram. Sau ɗaya a shekara uku rundunar jiragen ruwa na Tarshish sukan kawo zinariya, da azurfa, da hauren giwa, da birai, da ɗawusu masu daraja.


“‘Tarshish abokiyar cinikinki ce, saboda yawan dukiyarki ta sayi kayan cinikinki da azurfa, da baƙin ƙarfe, da kuza, da darma.


Sarakunan Esbanya da na tsibirai, Za su ba shi kyautai, Sarakunan Arabiya da na Habasha Za su kawo masa kyautai.


Ku yi ruri da baƙin ciki, ku jama'ar bakin teku, ku yi ƙoƙari ku tsere zuwa Tarshish!


An yi filafilan jirgin ruwanki da lilin mai kyau, mai ado daga Masar, Don ya zama alama. An yi tutar jirgin ruwanki da shuɗi da shunayya na gaɓar tekun Elisha.


Amma maimakon Yunusa yă tafi, sai ya gudu daga wurin Ubangiji zuwa Tarshish. Ya tafi Yafa, nan ya sami jirgin ruwa yana gab da tashi zuwa Tarshish, ya kuwa biya kuɗinsa, ya shiga tare da masu jirgin zuwa can don yă tsere wa Ubangiji.


Tasa ta ƙare, shi wanda ya ce da abin da aka yi da itace, ‘Farka!’ Ya kuma ce wa dutse wanda ba ya ji, ‘Tashi!’ Wannan zai iya koyarwa? Ga shi, an dalaye shi da zinariya da azurfa, Ba ya numfashi ko kaɗan.


Sau ɗaya a shekaru uku, sarki yakan aika da jiragen ruwa zuwa Tarshish tare da barorin Hiram, su kawo zinariya, da azurfa, da hauren giwa, da manyan birai, da ɗawisu.


Ai, mai aikin hannu ne ya yi shi a Isra'ila! Gunki ne ba Allah ba ne. Za a farfashe siffar maraƙin Samariya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ