“Ina amfanin gunki sa'ad da mai yinsa ya siffata shi? Shi siffa ne da aka yi da ƙarfe, mai koyar da ƙarya. Gama mai yinsa yakan dogara ga abin da ya siffata, Sa'ad da ya yi bebayen gumaka.
Masu ƙera gumaka ba su da ko tunanin da za su ce, “Na ƙone wani sashi na itacen nan. Na toya gurasa a garwashin, na kuma gasa nama, na ci shi, na kuwa ce sauran itacen zan sassaƙa gunki da shi. Ga ni yanzu, ina ta rusunawa gaban guntun itace!”
Ubangiji ya ce, “Mutanena wawaye ne, Ba su san ni ba, Yara ne dakikai, Ba su da ganewa. Suna gwanance da aikin mugunta, Amma ba su san yadda za su yi nagarta ba.”
Waɗanda suka ce wa itace, ‘Kai ne mahaifinmu.’ Suna kuma ce wa dutse, ‘Kai, ka haife mu.’ Gama sun ba ni baya, ba su fuskance ni ba. Amma sa'ad da suke shan wahala, sukan ce, ‘Ka zo ka taimake mu.’
Mutanena sukan yi tambaya a wurin abin da aka yi da itace, Sandansu yakan faɗa musu gaiɓu, Gama ruhun karuwanci ya ɓad da su, Sun rabu da Allahnsu don su yi karuwanci.