Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 10:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Kowane mutum dakiki ne, marar ilimi, Kowane maƙerin zinariya zai sha kunya saboda gumakansa, Gama siffofinsa ƙarya ne, Ba numfashi a cikinsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Kowa marar azanci ne, marar ilimi; kowane maƙerin zinariya zai sha kunya saboda gumakansa. Siffofinsa ƙarya ne; ba su da numfashi a cikinsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 10:14
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Dukansu dakikai ne wawaye, Koyarwar gumaka ba wani abu ba ne, itace ne kawai!


Dukan waɗanda suke dogara ga gumaka, Masu kiran siffofi allolinsu, Za a ƙasƙantar da su, su kuma sha kunya.”


Su waɗanda suka yi gumaka, dukansu za su sha kunya, Dukansu za su zama abin kunya.


Dukan waɗanda suke yi wa siffofi sujada za su sha kunya, Haka kuma waɗanda suke fāriya da gumakansu. Dukan alloli za su rusuna a gabansa.


Dukan wanda ya yi mata sujada za a ƙasƙantar da shi. Mutanen da suka ƙera gumakan, 'yan adam ne, ba wani abu ba. Bari su zo su tsaya gaban shari'a, za su razana, su kuma sha kunya.


Daga Sama Ubangiji ya dubi mutane, Yă ga ko da akwai masu hikima Waɗanda suke yi masa sujada.


Ga wani abin da wawa ba zai iya sani ba, Dakiki kuma ba zai iya ganewa ba,


Ya jama'ata, ƙaƙa kuka zama dakikai, wawaye haka? Sai yaushe za ku koya?


“Hakika wautata ta sa na zama kamar dabba ba mutum ba, Ba ni kuwa da fahimi irin na mutum.


saboda sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, har yi wa halitta ibada, sun kuma bauta mata, sun ƙi su yi wa Mahalicci, shi wanda yabo ya tabbata a gare shi har abada. Amin.


Gumakansu dodon gona suke, a cikin gonar kabewa, Ba su iya yin magana, Ɗaukarsu ake yi domin ba su iya tafiya! Kada ku ji tsoronsu. Gama ba su da ikon aikata mugunta ko alheri.”


Kashegari da safe kuma da suka tashi, sai suka ga Dagon ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Kan Dagon da hannuwansa a gutsure, suna nan a dokin ƙofa. Gangar jikin ce ta ragu.


Zan ba da labarin adalcinku da ayyukanku, amma ba za su taimake ku ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ