Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 10:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Sa'ad da ya yi murya akan ji ƙugin ruwa a cikin sammai Yakan kawo ƙasashi daga ƙurewar duniya, Yakan yi walƙiyoyi saboda ruwan sama, Daga cikin taskokinsa yakan kawo iska.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Sa’ad da ya yi tsawa, ruwaye a cikin sammai sukan yi ƙugi; yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya. Yakan aiki walƙiya da ruwan sama ya fitar da iska daga gidajen ajiyarsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 10:13
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yakan kawo gizagizan hadiri daga bangayen duniya, Yakan yi walƙiya domin hadura, Yakan fito da iska daga cikin taskarsa.


“Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara? Ko kuwa ka taɓa shiga rumbunan ajiyar ƙanƙara?


Sa'an nan Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama, Aka ji muryar Maɗaukaki. Ƙanƙara da garwashin wuta suka sauko.


Ya shimfiɗa gajimare a sararin al'arshi. Ya tanada wa duniya ruwan sama, Ya sa ciyayi su tsiro a kan tuddai.


Suna da kunnuwa, amma ba sa ji, Ba kuma numfashi a bakinsu.


Shi wanda ya hau cikin sararin sama, Daɗaɗɗen sararin sama! Ku kasa kunne ga muryarsa mai ƙarfi!


Iliya kuwa ya ce wa Ahab, “Sai ka haura ka ci ka sha, gama akwai motsin sakowar ruwan sama.”


Sai Musa ya miƙa sandansa sama, Ubangiji kuwa ya aiko da tsawa da ƙanƙara, wuta kuwa ta bi ƙasar. Ubangiji ya sa aka yi ƙanƙara a bisa ƙasar Masar.


Ku roƙi ruwan sama daga wurin Ubangiji a lokacin bazara, Gama Ubangiji ne yake yin gizagizan hadiri, Shi ne yake bai wa mutane yayyafi. Shi ne kuma yake ba kowane mutum tsire-tsiren saura.


a sa'an nan ba tsire-tsiren saura a duniya, ƙananan ganyayen saura kuma ba su riga sun tsiro ba, gama Ubangiji Allah bai sa a yi ruwa bisa duniya ba tukuna. A lokacin kuwa babu wani wanda zai noma ƙasar,


Daga sararin sama kakan aiko da ruwa bisa duwatsu, Ƙasa kuwa takan cika da albarkunka.


Bisa ga umarninsa ruwan da yake samaniya yakan yi ruri, Yakan sa gajimare su tashi daga ƙarshen duniya, Yakan sa walƙiya ta walƙata cikin ruwan sama, Yakan sa iska ta haura daga cikin taskokinsa.


Allah ne ya yi duwatsu Ya kuma halicci iska. Ya sanar da nufinsa ga mutum, Ya juya rana ta zama dare. Yana sarautar duniya duka. Sunansa kuwa Ubangiji Maɗaukaki!


A zuciya ba su cewa, ‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu Wanda yake ba mu ruwan sama a kan kari, Na kaka da na bazara, Wanda yake ba mu lokacin girbi.’


A cikin gumakan al'ummai akwai mai iya sa a yi ruwa? Sammai kuma su yi yayyafi? Ashe, ba kai ne ba, ya Ubangiji Allahnmu? Domin haka a gare ka muke sa zuciya, Gama kai ne mai yin waɗannan abubuwa duka.”


Haka zai yi wa wurin nan da mazauna cikinsa, ya mai da birnin nan kamar Tofet.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ