Saboda wannan ne kuma muke gode wa Allah ba fasawa, domin sa'ad da kuka karɓi Maganar Allah ta bakinmu, ba ku karɓe ta kamar maganar mutum ce ba, sai dai ainihin yadda take, Maganar Allah, wadda take aiki a cikin zuciyarku, ku masu ba da gasikya.
Domin haka, sai ka kasa kunne ga abin da Ubangiji ya ce. Saboda ka ce mini in daina yin annabci gāba da jama'ar Isra'ila, kada kuwa in yi wa zuriyar Ishaku ɓaɓatu,
Ya ku mutanen Isra'ila, ku ji maganar Ubangiji, Gama Ubangiji yana da shari'a da ku, ku mazaunan ƙasar. “Gama ba gaskiya, ko ƙauna, Ko sanin Ubangiji a ƙasar.
To, sai ku ji maganar Ubangiji, ya ku sauran mutanen Yahuza, Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, ‘Idan zuwa Masar kuka sa gaba don ku tafi ku zauna a can,
ka ce, ‘Ka ji maganar Ubangiji, ya Sarkin Yahuza, kai da kake zaune kan gadon sarautar Dawuda kai da barorinka, da mutanenka waɗanda suke shiga ta ƙofofin nan.
Ya Urushalima sarakunanki da jama'arki sun zama kamar Saduma da Gwamrata. Ku kasa kunne ga abin da Ubangiji yake faɗa muku. Ku mai da hankali ga abin da Allahnmu yake koya muku.
Makaiya kuwa ya ce, “Ka ji maganar Ubangiji, gama na ga Ubangiji yana zaune a kursiyinsa. Dukan taron mala'ikun Sama suna tsaye a wajen damansa da na hagunsa.
da Masar, da Yahuza, da Edom, da 'ya'yan Ammon, maza, da na Mowab, da dukan waɗanda suke zaune a hamada, da waɗanda suke yi wa kansu sanƙo, gama dukan al'umman nan marasa kaciya ne, dukan jama'ar Isra'ila kuma marasa kaciya ne a zuci.”
Ubangiji, wanda yake mulkin Isra'ila, ya kuma fanshe su, Ubangiji Mai Runduna, yake faɗar wannan, “Ni ne farko, da ƙarshe, Allah Makaɗaici, Ba wani Allah sai ni.