Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 1:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Amma Ubangiji ya ce mini, “Kada ka ce kai yaro ne, Kai dai ka tafi wurin mutanen da zan aike ka,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Amma Ubangiji ya ce mini, “Kada ka ce, ‘Ni ɗan yaro ne kawai.’ Dole ka je wurin kowane mutumin da na aike ka ka kuma faɗa abin da na umarce ka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 1:7
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sal Allah ya je wurin Bal'amu da dare, ya ce masa, “Idan mutanen nan sun zo kiranka ne, sai ka tashi, ka tafi tare da su, amma abin da na umarce ka kaɗai za ka yi.”


kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”


Amma sa'ad da na yi magana da kai, zan buɗe bakinka, kai kuwa za ka yi musu magana, ka ce, ‘Ubangiji ya ce, wanda zai ji, to, ya ji, wanda kuma zai ƙi ji, ya ƙi ji,’ gama su 'yan tawaye ne.”


Amma Mikaiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji abin da Allahna ya faɗa mini, shi zan faɗa.”


Amma Mikaiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji, abin da Ubangiji ya faɗa mini, shi ne zan faɗa.”


Bal'amu ya amsa wa Balak ya ce, “To, ai, ga shi, na zo yanzu! Ina da wani ikon yin wata magana ne? Maganar da Allah ya sa a bakina, ita zan faɗa, tilas.”


domin ban ji nauyin sanar da ku dukan nufin Allah ba.


Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka naɗa ni sarki, a matsayin Dawuda, tsohona, ko da yake ni yaro ne ƙarami, ban ƙware ba.


“Saboda haka za ka faɗa musu waɗannan abubuwa duka, amma ba za su ji ka ba. Za ka kira su, amma ba za su amsa ba.


Za ka faɗa musu maganata, ko su ji, ko kada su ji, gama su 'yan tawaye ne.


Amma Ubangiji ya raba ni da aikina na kiwo, ya umarce ni in tafi in yi magana da jama'arsa, wato Isra'ila.


“Ni ne Ubangiji, sai ka faɗa wa Fir'auna, Sarkin Masar, dukan abin da na faɗa maka.”


“Ka tsaya a filin Haikalin Ubangiji, ka yi wa dukan biranen Yahuza magana, su waɗanda suka zo Haikalin Ubangiji domin su yi sujada. Ka faɗa musu dukan maganar da na umarce ka, kada ka rage ko ɗaya.


Sa'ad da Irmiya ya gama faɗa wa dukan jama'a maganar da Ubangiji Allahnsu ya aiko musu da ita,


“Ka tashi ka tafi Nineba, babban birnin nan, ka yi musu shelar saƙon da zan faɗa maka.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ