Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 1:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Sai Ubangiji ya tambaye ni, ya ce, “Irmiya, me ka gani?” Na amsa, na ce, “Sandan itacen almond.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Me ka gani, Irmiya?” Sai na amsa na ce, “Na ga reshen itacen almon.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 1:11
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya tambaye ni, ya ce, “Amos, me ka gani?” Sai na ce, “Igiyar awon gini na gani.” Ya kuma ce, “Duba, da wannan zan nuna yadda jama'ata sun zama kamar bangon da ya karkace. Ba zan sāke nufina a kan yi musu hukunci ba.


Sai Ubangiji ya ce, “Amos, me ka gani?” Na ce, “Kwandon ɓaure na ci.” Ubangiji kuma ya ce mini, “Ƙarshen jama'ata Isra'ila ya zo. Ba zan sāke nufina a kan yi musu hukunci ba.


Sai mala'ikan ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?” Na amsa, “Na ga littafi mai tashi a sama, tsawonsa kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu goma.”


Sa'an nan ya ce mini, “Me ka gani?” Sai na ce, “Na ga alkuki wanda aka yi da zinariya tsantsa, da kwano a kansa, da fitilu bakwai a kansa, da butoci bakwai a kan kowace fitilar da yake bisa alkukin.


Sai Ubangiji ya ce mini, “Irmiya, me ka gani?” Sai na ce, “'Ya'yan ɓaure, akwai masu kyau ƙwarai, akwai kuma marasa kyau ƙwarai, har da ba za su ciwu ba.”


Kashegari Musa ya shiga alfarwar, sai ga shi, sandan Haruna na gidan Lawiyawa ya huda, ya yi toho, ya yi furanni, ya kuma yi 'ya'yan almon nunannu, wato wani irin itace ne mai kama da na yazawa.


“Ga rana ta zo. Ƙaddararku ta zo, rashin gaskiya ta yi fure, girmankai kuma ya yi toho.


Yakubu ya samo ɗanyun tsabgogin aduruku, da na katambiri, da na durumi, ya ɓare ya bayyanar da fararen zane-zanensu a fili.


To, haka maganar da na faɗa take, Ba ta kāsa cika abin da na shirya mata, Za ta yi kowane abin da na aike ta ta yi.


Gama ni Ubangiji zan yi magana, maganata kuwa za ta tabbata, ba za ta yi jinkiri ba, amma za ta tabbata a kwanakinku, ku 'yan tawaye. Zan yi magana, za ta kuwa tabbata, ni Ubangiji Allah, na faɗa.”


Domin haka ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji na ce maganata ba za ta yi jinkiri ba, amma maganar da na faɗa za ta tabbata, ni Ubangiji Allah, na faɗa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ