Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 9:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Alkawarin farko yana da ka'idodinsa na yin sujada, da kuma wurin yinta tsattsarka wanda mutane suka shirya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Alkawarin farko ya ƙunshi ƙa’idodi don sujada da kuma tsattsarkan wuri a duniya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 9:1
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Za su yi tsattsarkan wuri domina, don in zauna tare da su.


mai hidima a Wuri Mafi Tsarki, da kuma masujada ta gaskiya, wadda Ubangiji ya kafa, ba mutum ba.


Ubangiji kuma ya ce, “Don haka sai ku kiyaye umarnina, kada ku kiyaye dokoki na banƙyama waɗanda aka kiyaye kafin ku zo, kada ku ƙazantu da su. Ni ne Ubangiji Allahnku.”


“Domin haka sai su kiyaye umarnaina don kada su yi zunubi su mutu ta wurin karya tsarkakakkun ka'idodina. Ni ne Ubangiji, ni na sa su tsarkaka.


Domin da wancan alkawari na farko bai gaza da kome ba, da ba sai an sāke neman na biyu ba.


Ku lura fa, kada kowa ya ribace ku ta hanyar iliminsa na yaudarar wofi, bisa ga al'adar mutane kawai, wato, bisa ga al'adun duniyar nan, ba bisa ga koyarwar Almasihu ba.


Idan sun ji kunyar dukan abin da suka aikata, sai ka nuna musu fasalin Haikalin, da tsarinsa, da wuraren fita, da wuraren shiga, da fasalinsa duka. Ka kuma sanashe su dukan ka'idodinsa, da dukan dokokinsa. Ka rubuta a gaban idanunsu don su kiyaye, su aikata dukan dokokinsa da dukan ka'idodinsa.


Kada su bar kome daga cikinsa ya kai gobe, kada kuwa a fasa ƙashinsa, sai su yi shi bisa ga dukan umarnin Idin Ƙetarewa.


Da ya ce sabon alkawari, ashe kuwa, ya mai da na farkon tsoho ke nan. Abin da yake tsufa, yana kuwa daɗa tsofewa, lalle ya yi kusan shuɗewa ke nan.


Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna bin umarnin Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi.


Su ne Isra'ilawa. Da zama 'ya'yan Allah, da ganin ɗaukakarsa, da alkawaran nan, da baiwar Shari'a, da ibada, da kuma sauran alkawarai, duk nasu ne.


Domin Almasihu bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake sura ne kawai na gaskataccen, a'a Sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ