Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 8:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Suna bauta wa makamantan abubuwan Sama da kuma ishararsu, kamar yadda Allah ya gargaɗi Musa sa'ad da yake shirin kafa alfarwar nan, da ya ce, “Ka lura fa, ka shirya kome da kome daidai yadda aka nuna maka a kan dutsen.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Suna hidima a cikin tsattsarkan wuri wanda yake hoto da kuma siffar abin da yake cikin sama. Shi ya sa aka gargaɗi Musa sa’ad da yana dab da gina tabanakul cewa, “Ka lura fa, ka yi kome daidai bisa ga zānen da aka nuna maka a kan dutsen.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 8:5
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai ku lura, ku yi waɗannan abubuwa duka bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.”


Waɗannan kam, isharori ne kawai na abin da zai auku, amma Almasihu shi ne ainihinsu.


To, tun da yake Shari'a ishara ce kawai ta kyawawan abubuwan da suke a gaba, ba ainihin siffarsu ba, ashe, har abada ba za ta iya kammala waɗanda suke kusatar Allah ta wurin waɗannan hadayu ba, waɗanda ake yi a kai a kai kowace shekara.


Ta haka za ku yi alfarwar bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.


Sarki Dawuda ya ce, “Dukan wannan rubutacce ne daga wurin Ubangiji zuwa gare ni domin in fahimci fasalin aikin filla filla.”


Za ku yi bagaden da katakai, sa'an nan ku roɓe cikinsa. Ku yi shi bisa ga fasalin da na nuna maka bisa dutsen.


Ya kuma ba shi tsarin dukan abin da ya yi nufin yi, na filayen Haikalin Ubangiji da dukan ɗakuna na kewaye, da ɗakunan ajiya na Haikalin Allah, da ɗakunan ajiye kyautan da aka keɓe ga Ubangiji.


wadda take ishara ce ga wannan zamani. Bisa ga wannan ishara akan yi miƙa sadaka da hadaya, amma ba sa iya kammala lamirin mai ibadar,


Da zinariya aka ƙera alkukin tun daga samansa har gindinsa, bisa ga fasalin da Ubangiji ya nuna wa Musa.


Ku kula fa, kada ku ƙi mai maganar nan. Domin in waɗanda suka ƙi jin mai yi musu gargaɗi a duniya ba su tsira ba, to, ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi jin wannan da yake yi mana gargaɗi ma daga Sama?


Ta wurin bangaskiya Nuhu, da Allah ya yi masa gargaɗi a kan al'amuran da ba a gani ba a lokacin, yana tsoron Allah, ya sassaƙa jirgi, don ceton iyalin gidansa, ta wurin bangaskiya kuma ya tabbatar wa duniya laifinta, har ya zama magājin adalcin Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya.


“Dā kakanninmu suna da alfarwar shaida a jeji, irin wadda mai maganar nan da Musa ya umarta a yi, daidai fasalin da ya gani.


Za ku yi mazaunina da kayayyakinsa duka, bisa ga irin fasalin da zan nuna maka.”


Amma da aka gargaɗe su a mafarki kada su koma wurin Hirudus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.


Muna da bagadin hadaya, wanda masu ibada a alfarwar nan ba su da izini su ci abincin wurin,


Bayan wannan na duba, ga Wuri Mafi Tsarki a buɗe a Haikali a Sama.


Mun yi tunani, cewa idan wata rana aka ce mana, ko aka ce wa zuriyarmu haka, sai mu ce, ‘Ku dubi bagaden Ubangiji wanda iyayenmu suka gina, ba domin miƙa hadayu na ƙonawa, ko na sadaka ba, amma domin shaida a tsakaninmu da ku.’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ