Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 8:4 - Littafi Mai Tsarki

4 To, ashe, da har yanzu yana duniya, da bai zama firist ba ke nan, tun da yake akwai firistocin da suke miƙa sadakoki bisa ga Shari'a.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Da a ce yana a duniya ne, da bai zama firist ba, domin a nan akwai mutanen da doka ta naɗa don su miƙa baye-baye.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 8:4
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kowane babban firist, da yake an zaɓe shi ne daga cikin mutane, akan sa shi yă wakilci mutane ga al'amarin Allah, don yă miƙa sadakoki da kuma hadayu domin kawar da zunubai.


Ku lura da ayyukan Wuri Mai Tsarki da na bagade don kada hasala ta sāke fāɗa wa Isra'ilawa.


Zai zama abin tunawa ga Isra'ilawa domin kada wanda ba firist ba, ba kuwa a cikin zuriyar Haruna ba, ya guso don ya ƙona turare a gaban Ubangiji, domin kada ya zama kamar Kora da ƙungiyarsa. Haka Ubangiji ya faɗa wa Ele'azara ta bakin Musa.


Ta wurin bangaskiya Habila ya miƙa wa Allah hadaya mafi kyau a kan Kayinu, ta wurin wannan bangaskiya ce ya kuma sami yardar Allah a kan shi mai adalci ne domin Allah ma ya shaide shi, da ya karɓi abubuwan da ya bayar. Ya mutu kam, amma ta wurin bangaskiyar nan tasa har ya zuwa yanzu yana magana.


Ba zai miƙa hadaya kowace rana kumar waɗancan manyan firistocin ba, wato, da farko saboda zunubansa, sa'an nan kuma saboda na jama'a. Wannan ya yi ta ne sau ɗaya tak, lokacin da ya miƙa kansa hadaya.


Kowane babban firist akan sa shi domin ya miƙa sadakoki da hadayu, saboda haka wajibi ne wannan shi ma, ya zamanto yana da abin da zai miƙa.


wadda take ishara ce ga wannan zamani. Bisa ga wannan ishara akan yi miƙa sadaka da hadaya, amma ba sa iya kammala lamirin mai ibadar,


Har wa yau kuma, kowane firist yakan tsaya a kan hidimarsa kowace rana, yana miƙa hadaya iri ɗaya a kai a kai, waɗanda har abada ba za su iya ɗauke zunubai ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ