Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 8:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Ba kuma sai sun koya wa ɗan garinsu ba, Balle wani ya ce ɗan'uwansa, ‘Kă san Ubangiji!’ Domin kowa zai san ni, Daga ƙaraminsu, har ya zuwa babbansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa ba, balle mutum yă ce wa ɗan’uwansa, ‘Ka san Ubangiji,’ domin dukansu za su san ni, daga ƙaraminsu zuwa babba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 8:11
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa, ko ɗan'uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji’ ba, gama su duka za su san ni, tun daga ƙarami har zuwa babba. Zan gafarta musu laifofinsu, ba kuwa zan ƙara tunawa da zunubansu ba.”


“Ni kaina zan koya wa mutanenki, Zan kuwa ba su wadata da salama.


A rubuce yake cikin littattafan annabawa cewa, ‘Dukkansu Allah ne zai koya musu.’ To, duk wanda ya ji, ya kuma koya wurin Uba, zai zo gare ni.


Ku kam, shafar nan da kuka samu daga Ruhu Mai Tsarki tā tabbata a zuciyarku, ba sai wani ya koya muku ba. Amma kamar yadda shafar nan tasa take koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa.


Zan ba su zuciyar da za su sani ni ne Ubangiji. Za su kuwa zama jama'ata, ni kuwa zan zama Allahnsu, gama za su komo wurina da zuciya ɗaya.


Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami.


Duk jama'a kuwa suka mai da hankali a gare shi, babba da yaro, suna cewa, “Mutumin nan, ai, ikon nan ne na Allah, da ake kira mai girma.”


Duniya za ta cika da sanin ɗaukakar Ubangiji, Kamar yadda ruwa ya cika teku.


“Kai kuwa ɗana Sulemanu, sai ka san Allah na tsohonka, ka bauta masa da zuciya ɗaya, da kuma yardar rai, gama Ubangiji mai binciken dukan zukata ne, ya kuma san kowane irin nufi da tunani. Idan ka neme shi, za ka same shi, in kuwa ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada.


Jama'arsu za su ce, “Bari mu haura zuwa tudun Ubangiji, Zuwa ga Haikalin Allah na Isra'ila. Za mu koyi abin da yake so mu yi, Za mu yi tafiya a hanyar da ya zaɓa. Koyarwar Ubangiji daga Urushalima take zuwa, Daga Sihiyona yake magana da jama'arsa.”


Za su sani ni Ubangiji Allahnsu, ina tare da su, mutanen Isra'ila kuwa su ne mutanena, ni Ubangiji Allah na faɗa.


“Kai kuma, Ezra, bisa ga hikimar da Allahnka ya ba ka, sai ka naɗa mahukunta da alƙalai waɗanda za su yi wa mutanen da suke a lardin Yammacin Kogi shari'a, wato dukan waɗanda suka san shari'a. Waɗanda ba su san shari'a ba kuwa, sai ka koya musu.


Hezekiya kuwa ya yi magana ta ƙarfafawa ga dukan Lawiyawa waɗanda suka nuna fasaha a hidimar Ubangiji. Mutane fa suka ci abincin idin har kwana bakwai, suna miƙa hadayu na salama, suna ta yin godiya ga Ubangiji Allah na kakanninsu.


Sauran mutanen Yahuza kuwa waɗanda suka ragu, waɗanda suke niyyar zuwa ƙasar Masar da zama, zan sa dukansu su halaka a can. Takobi da yunwa za su kashe dukansu a Masar, da yaro da babba. Za su zama abin la'antawa, da abin tausayi, da abin zargi, da abin kunya.


Gama daga ƙaraminsu zuwa babba, Kowannensu yana haɗama ya ci ƙazamar riba, Har annabawa da firistoci, Kowannensu ya shiga aikata rashin gaskiya.


Shugabannin sojoji, da Yohenan ɗan Kareya, da Yazaniya ɗan Hoshaiya, da jama'a duka, daga ƙarami zuwa babba, suka zo,


Sai Irmiya ya kira Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji waɗanda suke tare da shi, da dukan jama'a tun daga ƙarami har zuwa babba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ