Ba shakka, asirin addininmu muhimmi ne ƙwarai, An bayyana shi da jiki, Ruhu ya nuna shi adali ne, Mala'iku sun gan shi, An yi wa al'ummai wa'azinsa, An gaskata da shi a duniya, An ɗauke shi Sama wurin ɗaukaka.
Da Dawuda ya komo gida domin ya sa wa iyalinsa albarka, Mikal, 'yar Saul, ta fito domin ta tarye shi, ta ce masa, “Ƙaƙa Sarkin Isra'ila ya ɗauki kansa yau? Ya kware darajarsa a gaban barorinsa mata kamar yadda shakiyyai suke yi.”
Waɗannan duka su ne kabilan Isra'ila goma sha biyu, wannan kuma shi ne abin da mahaifinsu ya faɗa musu sa'ad da yake sa musu albarka. Ya sa wa kowannensu albarka da irin albarkar da ta cancance shi.