Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 7:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Ba zai miƙa hadaya kowace rana kumar waɗancan manyan firistocin ba, wato, da farko saboda zunubansa, sa'an nan kuma saboda na jama'a. Wannan ya yi ta ne sau ɗaya tak, lokacin da ya miƙa kansa hadaya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 Ba ya bukata yă yi ta miƙa hadayu kowace rana saboda zunubansa, sa’an nan saboda zunuban mutane kamar sauran firistoci. Ya miƙa hadaya sau ɗaya tak, sa’ad da ya miƙa kansa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 7:27
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

shi Almasihu ma, da aka miƙa shi hadaya sau ɗaya tak, domin ya ɗauke zunuban mutane da yawa, zai sāke bayyana, bayyana ta biyu, ba a kan maganar kawar da zunubi ba, sai dai domin yă ceci waɗanda suke ɗokin zuwansa.


Almasihu ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak, ba ƙari, ba kuwa ta wurin jinin awaki ko na 'yan maruƙa ya shiga ba, sai dai ta wurin nasa jini, ya samo mana madawwamiyar fansa.


balle fa jinin Almasihu wanda ya miƙa kansa marar aibu ga Allah, ta wurin Madawwamin Ruhu, lalle zai tsarkake lamirinmu daga barin ibada marar tasiri, domin mu bauta wa Allah Rayayye.


Ku yi zaman ƙauna kamar yadda Almasihu ya ƙaunace mu, ya kuma ba da kansa dominmu, sadaka mai ƙanshi, hadaya kuma ga Allah.


Saboda haka, wajibi ne yă miƙa hadayu, ba saboda kawar da zunuban jama'a kaɗai ba, har ma don nasa.


wanda ya ba da kansa dominmu, domin ya fanso mu daga dukan mugun aiki, ya kuma tsarkake jama'a su zama abin mulkinsa, masu himmar yin kyakkyawan aiki.


Mutuwar nan da ya yi kuwa, ya mutu ne sau ɗaya tak ba ƙari, saboda shafe zunubanmu, amma rayuwar da yake yi, yana rayuwa ne, rayuwa ga Allah.


Ba kuwa domin ya riƙa miƙa kansa hadaya a kai a kai ba ne, kamar yadda babban firist yake shiga Wuri Mafi Tsarki a kowace shekara da jinin da ba nasa ba ne.


Haruna kuma zai miƙa bijimi na yin hadaya don zunubin kansa, ya yi kafara don kansa da gidansa. Zai yanka bijimi na yin hadaya don zunubin kansa.


Amma na biyun, sai babban firist kaɗai yake shiga, shi ma kuwa sai sau ɗaya a shekara, sai kuma da jini wanda yakan miƙa saboda kansa, da kuma kurakuran jama'a.


Kowane babban firist, da yake an zaɓe shi ne daga cikin mutane, akan sa shi yă wakilci mutane ga al'amarin Allah, don yă miƙa sadakoki da kuma hadayu domin kawar da zunubai.


Sai kuma ya yanka bunsuru na yin hadaya don zunubin jama'ar ya shigar da jinin bayan labulen. Zai sa jinin kamar yadda ya yi da jinin bijimin, ya yayyafa shi a kan murfin, da gaban murfin.


Haruna zai miƙa bijimi na yin hadaya don zunubi saboda kansa. Zai yi kafara don kansa da gidansa.


A cikinsa ne ku kuma aka gina ku, ku zama mazaunin Allah ta wurin Ruhu.


sai ka ba firistoci na zuriyar Zadok, masu yi mini hidima, bijimai na yin hadaya domin zunubi.


To, ashe, da har yanzu yana duniya, da bai zama firist ba ke nan, tun da yake akwai firistocin da suke miƙa sadakoki bisa ga Shari'a.


In da haka ne, ashe, da sai lalle ya yi ta shan wuya a kai a kai ke nan, tun daga farkon duniya. Amma a yanzu ya bayyana sau ɗaya tak, a ƙarshen zamanai, domin ya kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ