Haka kuma bayan jibin, sai ya ɗauki ƙoƙo, ya ce, “Ƙoƙon nan na Sabon Alkawari ne, da aka tabbatar da shi da jinina. Ku yi haka duk a sa'ad da kuke sha, domin tunawa da ni.”
Gama ni baranka na ɗauki lamunin saurayin wurin mahaifinsa da cewa, ‘In ban komo maka da shi ba, sai alhakinsa ya zauna a kaina a gaban mahaifina duka raina.’
Allah mai zartar da salama, wanda ya ta da Ubangijinmu Yesu, Makiyayin tumaki mai girma, daga matattu, albarkacin jinin nan na tabbatar madawwamin alkawari,
Wannan shugaba zai yi alkawari mai ƙarfi na shekara bakwai da mutane da yawa. Amma bayan shekara uku da rabi za a hana a yi sadaka da hadaya. Abin ƙyama zai kasance a ƙwanƙolin Haikali, har lokacin da ƙaddara za ta auko wa wanda ya sa abin ƙyama.”