Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 7:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Waɗancan sun zama firistoci, ba tare da an yi musu rantsuwa ba, amma wannan kam, sai da aka yi masa rantsuwa, da Allah ya ce masa, “Ubangiji ya rantse, Ba kuwa zai ta da maganarsa ba cewa, ‘Kai firist ne har abada.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 shi wannan ya zama firist ta wurin rantsuwar da Allah ya yi da ya ce masa, “Ubangiji ya rantse, ba kuwa zai canja zuciyarsa ba, ‘Kai firist ne na har abada.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 7:21
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji ya yi muhimmin alkawari, Ba kuwa zai fasa ba! “Za ka zama firist har abada Bisa ga tsabi'ar Malkisadik firist.”


Domin an shaide shi da cewa, “Kai firist ne na har abada, Kwatancin ɗabi'ar Malkisadik.”


Gama Maɗaukaki na Isra'ila ba zai yi ƙarya, ko ya sāke nufinsa ba. Shi ba mutum ba ne, da zai sāke nufinsa.”


Allah ba kamar mutum ba ne, da zai yi ƙarya, Ba kuwa ɗan mutum ba ne, da zai tuba. Zai cika dukan abin da ya alkawarta, Ya hurta, ya kuwa cika.


Domin baiwar Allah da kiransa ba sa tashi.


Kamar dai yadda a wani wuri kuma ya ce, “Kai firist ne na har abada, Kwatancin ɗabi'ar Malkisadik.”


Waɗancan firistoci, an yi su da yawa, domin mutuwa ta hana su tabbata a aikin.


Wato shari'a tana sa mutane su zama manyan firistoci duk da rauninsu, amma maganar nan ta rantsuwa da ta sauko bayan Shari'a, ta sa Ɗa wanda yake kammalalle har abada.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ