Ibraniyawa 7:19 - Littafi Mai Tsarki19 don Shari'a ba ta kammala kome ba, ta wani hali kuma an shigo da wani bege wanda yake mafi kyau, ta wurinsa kuwa muke kusatar Allah. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202019 (gama doka ba tă mai da wani abu cikakke ba), yanzu kuwa bege mafi kyau ya ɗauki matsayinta. Ta haka kuma muka matso kusa da Allah. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
da yake mun sani mutum ba ya samun kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari'a, sai dai ta wurin gaskatawa ga Yesu Almasihu kaɗai, mu ma mun gaskata da Almasihu Yesu, domin mu sami kuɓuta ga Allah ta wurin bangaskiya ga Almasihu, ba ta wurin bin Shari'a ba, don ba ɗan adam ɗin da zai sami kuɓuta ga Allah ta hanyar bin Shari'a.