Abin da ba shi yiwuwa Shari'a ta yi domin ta kasa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi a cikin jiki, da ya aiko da Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi.
Amma a yanzu da kuka san Allah, ko ma dai a ce Allah ya san ku, ta yaya za ku sāke komawa a kan raunanan al'adu marasa biyan bukata, har kuna neman komawa ga bautarsu?
Kada baƙuwar koyarwa iri iri ta bauɗar da ku, ai, abu ne mai kyau alherin Allah ya zamana shi yake ƙarfafa zuciya, ba abinci iri iri ba, waɗanda ba su amfani ga masu dogara da su.
Ga abin da nake nufi. Shari'ar nan, wadda ta zo shekara arbaminya da talatin daga baya, ba ta shafe alkawarin nan da Allah ya tabbatar tun tuni ba, har da za ta wofinta shi.
To, 'yan'uwa, bari in yi muku misali. Ko alkawari na mutum ne kawai, in dai an riga an tabbatar da shi, ba mai soke shi, ba kuma mai ƙara wani abu a kai.
Wato, Shari'a ta zama saɓanin alkawaran Allah ke nan? A'a, ko kusa! Domin da an ba da wata shari'a mai iya ba da rai, da sai a sami adalcin Allah ta hanyar bin Shari'ar nan.