Sa'an nan za ki tuna da ayyukanki, ki ji kunya, sa'ad da na ɗauki yarki da ƙanwarki, na ba ki su, su zama 'ya'yanki mata, amma ba a kan alkawarin da na yi da ke ba.
Gama da a ce kammala tana samuwa ta wurin firistoci na zuriyar Lawi (don ta gare su ne jama'a suka karɓi shari'a), wace bukata kuma ake da ita ta wani firist dabam ya bayyana kwatancin ɗabi'ar Malkisadik, wanda za a ambata ba kwatancin ɗabi'ar Haruna ba?