Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 6:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Ko da yake mun faɗi haka, a game da ku kam, ya ƙaunatattu, mun tabbata kuna a kan abubuwa mafiya kyau na zancen ceto.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Abokaina, ko da yake muna irin maganan nan, mun tabbata kuna yi abubuwan nan masu kyau da waɗanda suka sami ceto suke yi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 6:9
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma mu ba a cikin waɗanda suke ja da baya su hallaka muke ba, mu a cikin masu bangaskiya muke, mai kai mu ga ceton rayukanmu.


to, ta ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi kula da ceto mai girma haka? Domin Ubangiji kansa, shi ne ya fara sanar da shi, waɗanda suka saurare shi kuma suka tabbatar mana da shi,


Don baƙin ciki irin wanda Allah yake sawa, shi ne yake biyarwa zuwa ga tuba, da kuma samun ceto, ba ya kuma sa “da na sani”. Amma baƙin ciki a kan al'amarin duniya, yakan jawo mutuwa.


domin kun ji tausayin ɗaurarru, kun kuma yarda da daɗin rai da wason da aka yi muku, tun da yake kun sakankance kuna da mallaka mafi kyau, mai tabbata kuwa.


da ya kai ga kammala, sai ya zama tushen madawwamin ceto ga dukkan waɗanda suke masa biyayya,


Saboda haka, ya ƙaunatattuna, ku guji bautar gumaka.


ina tabbatar wa Yahudawa da al'ummai duka sosai wajibcin tuba ga Allah, da kuma gaskatawa da Ubangijinmu Yesu.


Duk wanda ya ba da gaskiya, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma wanda ya ƙi ba da gaskiya za a hukunta shi.


Gama haka wanda yake can Sama, Maɗaukaki, wanda ake kira Mai Tsarki ya ce, “Ina zaune a can Sama a tsattsarkan wuri, tare kuma da wanda yake da halin tuba mai tawali'u, don in farfaɗo da ruhun masu tawali'u, in kuma farfaɗo da zukatan masu tuba.


Gama Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi, wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi.


In muna a cikin Almasihu Yesu, kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba. Bangaskiya mai aikata ƙauna ita ce wani abu.


Da suka ji haka, suka rasa ta cewa, suka kuma ɗaukaka Allah suka ce, “Ashe, har al'ummai ma Allah ya ba su tuba zuwa rai.”


Ya ku ƙaunatattu, tun da aka yi mana waɗannan alkawarai, sai mu tsarkake kanmu daga kowace irin ƙazanta ta jiki ko ta zuci, da bangirma ga Allah mu kamalta a cikin tsarki.


Ashe, tun dā tsammani kuke yi muna kawo hanzarinmu a gare ku ne? A'a, a gaban Allah muke magana, muna na Almasihu, wannan kuwa duk domin inganta ku ne, ya ku ƙaunatattu.


Ya ƙaunatattuna, ina roƙonku don ku baƙi ne, bare kuma, ku guje wa mugayen sha'awace-sha'awace na halin mutuntaka waɗanda suke yaƙi da zuciyarku.


Ya ƙaunatattuna, wannan ita ce wasiƙa ta biyu da na rubuto muku, a kowaccensu kuwa na faɗakar da sahihan zukatanku ta hanyar tuni.


Ya ku ƙaunatattuna, ba fa wani sabon umarni nake rubuto muku ba, a'a, daɗaɗɗen umarnin nan ne wanda kuke da shi tun farko. Daɗaɗɗen umarnin nan kuwa, ai, shi ne maganar da kuka ji.


Ya ku ƙaunatattuna, da yake dā ma ina ɗokin rubuto muku zancen ceton nan namu, mu duka, sai na ga wajibi ne in rubuto muku in gargaɗe ku, ku dage ƙwarai a kan bangaskiyar nan da aka danƙa wa tsarkaka sau ɗaya tak, ba ƙari.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ