Na kan dutsen kuwa su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar, sai su karɓa da farin ciki. Su kam, ba su da tushe. Sukan ba da gaskiya 'yan kwanaki kaɗan, amma a lokacin gwaji, sai su bauɗe.
In kuwa bayan da suka tsere wa ƙazantar duniyar albarkacin sanin Ubangijinmu, Mai Cetonmu Yesu Almasihu, suka kuma sāke sarƙafewa a ciki, har aka rinjaye su, ƙarshen zamansu ya fi na fari lalacewa ke nan.
don Hirudus yana tsoron Yahaya, ya sani shi mutum ne adali, tsattsarka, shi ya sa ya kāre shi. Hirudus yakan damu da yawa sa'ad da yake sauraron Yahaya, ko da yake na murna da jinsa.
Domin Maganar Allah rayayyiya ce, mai ƙarfin aiki, ta fi kowane irin takobi kaifi, har tana ratsa rai da ruhu, da kuma gaɓoɓi, har ya zuwa cikin ɓargo, tana kuma iya rarrabe tunanin zuciya da manufarta.