Ka tuna da bayinka Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, waɗanda kai da kanka ka rantse musu, ka ce, ‘Zan riɓaɓɓanya zuriyarku kamar taurarin sama, in kuma ba ku wannan ƙasa duka da na alkawarta zan bayar ga zuriyarku. Za su kuwa gāje ta har abada’ ”
ya ce mini, ‘Ga shi, zan sa ka hayayyafa, in riɓaɓɓanya ka, zan maishe ka ƙungiyar al'ummai, zan kuwa ba da wannan ƙasa ga zuriyarka a bayanka ta zama madawwamiyar mallaka.’
Duba, na sa ƙasar a gabanku, sai ku shiga ku mallake ta, ƙasa wadda na rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, cewa zan ba su, su da zuriyarsu a bayansu.’ ”