amma Almasihu mai aminci ne, yana mulkin jama'ar Allah a kan shi Ɗa ne, mu ne kuwa jama'arsa, muddin mun tsaya gabanmu gaɗi, muna gadara da begenmu ƙwarai.
Domin kuwa wane ne a cikin mala'iku Allah ya taɓa ce wa, “Kai Ɗana ne, Ni Ubanka ne yau”? da kuma, “Zan kasance Uba a gare shi, Shi kuma, zai kasance Ɗa a gare ni”?
Amma aka yi masa rauni saboda zunubanmu, Aka daddoke shi saboda muguntar da muka aikata. Hukuncin da ya sha ya 'yantar da mu, Dūkan da aka yi ta yi masa, ya sa muka warke.