Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 5:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Ba wanda zai kai kansa wannan matsayi mai girma, sai dai Allah ya yi kiransa ga haka, kamar yadda aka kirayi Haruna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Ba wanda yakan kai kansa a wannan matsayi mai girma; sai ko Allah ya kira shi, kamar yadda aka yi wa Haruna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 5:4
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Daga cikin 'ya'ya maza na Isra'ila sai ka kirawo ɗan'uwanka Haruna tare da 'ya'yansa, Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar, su zama firistoci masu yi mini aiki.


Zai zama abin tunawa ga Isra'ilawa domin kada wanda ba firist ba, ba kuwa a cikin zuriyar Haruna ba, ya guso don ya ƙona turare a gaban Ubangiji, domin kada ya zama kamar Kora da ƙungiyarsa. Haka Ubangiji ya faɗa wa Ele'azara ta bakin Musa.


Sa'an nan ya ce wa Kora da ƙungiyarsa, “Da safe Ubangiji zai nuna mana wanda yake nasa, zai sa wanda yake nasa, wato wanda ya zaɓa, ya sadu da shi a bagade.


Sai suka hana sarki Azariya, suka ce masa, “Ba aikinka ba ne, Azariya, ka ƙona turare ga Ubangiji, wannan aikin firistoci ne, 'ya'yan Haruna, waɗanda aka keɓe su don ƙona turare. Fita daga wurin nan mai tsarki, gama ka yi kuskure, ba za ka sami daraja daga wurin Ubangiji Allah ba.”


'Ya'yan Amram, maza, su ne Haruna, da Musa. Aka keɓe Haruna domin ya tsarkake abubuwa mafi tsarki, domin shi da 'ya'yansa za su ƙone turare a gaban Ubangiji, su yi masa hidima, su riƙa sa albarka da sunansa har abada.


Sai Yahaya ya amsa ya ce, “Ba mai iya samun kome sai ko an ba shi daga Sama.


Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji ta cinye mutum ɗari biyu da hamsin ɗin nan da suke miƙa hadaya da turare.


Da kai, da 'ya'yanka za ku yi aikin firist da duk abin da ya shafi bagade da aiki na bayan labule. Ku ne za ku yi wannan aiki. Na ba ku aikin firist ya zama naku. Duk wani dabam wanda ya zo kuwa, za a kashe shi.”


Ya yarda ka zo kusa da shi, kai da dukan 'yan'uwanka Lawiyawa, a yanzu kuwa sai ƙoƙari kuke ku karɓi aikin firist!


Ku zuba wuta a ciki, ku kuma zuba musu turaren wuta a gaban Ubangiji. Sa'an nan ne za mu ga wanda Ubangiji ya zaɓa tsakaninmu. Ku Lawiyawa ku ne kuka fi fiffiƙewa!”


“Ɗauki Haruna da 'ya'yansa maza, da rigunan, da man keɓewa, da bijimi na yin hadaya don zunubi, da raguna biyu, da kwandon abinci marar yisti.


Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Haruna, maza, da aka naɗa firistoci domin su yi aikin firist.


da Abishuwa da Finehas, da Ele'azara, da Haruna babban firist.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ