10 gama Allah yana kiransa Babban Firist, kwatancin ɗabi'ar Malkisadik.
10 Allah kuwa ya naɗa shi yă zama babban firist, bisa ga tsarin Melkizedek.
a inda saboda mu ne Yesu ya riga mu shiga, da yake ya zama Babban Firist na har abada, kwatancin ɗabi'ar Malkisadik.
Sai Malkisadik Sarkin Salem, wato Urushalima, ya kawo gurasa da ruwan inabi. Shi firist ne na Allah Maɗaukaki.
Ubangiji ya yi muhimmin alkawari, Ba kuwa zai fasa ba! “Za ka zama firist har abada Bisa ga tsabi'ar Malkisadik firist.”
Saboda haka, lalle ne yă zama kamar 'yan'uwansa ta kowane hali, domin yă zama Babban Firist, mai jinƙai, mai aminci kuma na al'amarin Allah, yă kuma miƙa hadayar sulhu ta gafarta zunuban jama'a.
Saboda haka, ya ku 'yan'uwa tsarkaka, ku da kuke da rabo a kiran nan basamaniya, sai ku tsai da zuciya ga Yesu, Manzo, da kuma Babban Firist na bangaskiyar da muke shaidawa,
Muna da abu da yawa da za mu faɗa a game da shi kuwa, amma zai yi wuyar bayani, da yake basirarku ta dushe.