Rana tana zuwa sa'ad da sabon sarki zai fito daga cikin gidan sarautar Dawuda, zai zama alama ga sauran al'umma. Za su tattaru a birnin sarautarsa su girmama shi.
Mu kuwa da muka ba da gaskiya, muna shiga inuwar, yadda ya ce, “Sai na yi rantsuwa da fushina, na ce, ‘ba za su shiga inuwata ba sam,’ ” ko da yake ayyukan Allah gamammu ne tun daga farkon duniya.
Sai kuma na ji wata murya daga Sama tana cewa, “Rubuta wannan. Albarka tā tabbata ga matattu, wato, waɗanda za su mutu a nan gaba a kan su na Ubangiji ne.” Ruhu ya ce, “Hakika, masu albarka ne, domin su huta daga wahalarsu, gama aikinsu yana a biye da su!”