Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 4:7 - Littafi Mai Tsarki

7 to, sai ya sāke sa wata rana, ya ce, “Yau,” yana magana ta bakin Dawuda bayan da aka daɗe, kamar an riga an faɗa cewa, “Yau in kun ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Saboda haka Allah ya sāke sa wata rana, yana kiranta Yau, bayan wani dogon lokaci Allah ya yi magana ta bakin Dawuda, yadda aka riga aka faɗa, “Yau, in kuka ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 4:7
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Shi ne Allahnmu, Mu ne jama'ar da yake lura da ita, Mu ne kuma garken da yake ciyarwa. Yau ku ji abin da yake faɗa.


Domin kuwa an ce, “Yau in kun ji muryarsa, Kada ku taurare zukatanku kamar a lokacin tawayen nan.”


Ya ce musu, “To, yaya kuwa Dawuda, ta ikon Ruhu, ya ce da shi Ubangiji? Har ya ce,


Da suka kasa yarda a junansu, kafin su watse sai Bulus ya yi musu magana ɗaya ya ce, “Ashe kuwa, Ruhu Mai Tsarki daidai ya faɗa, da ya yi wa kakanninku magana ta bakin Annabi Ishaya cewa,


sai ya hango, ya kuma yi faɗi a kan tashin Almasihu daga matattu, cewa ba za a yashe shi a Hades ba, jikinsa kuwa ba zai ruɓa ba.


Domin Dawuda da kansa a Zabura ya ce, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, Zauna a damana,


Domin Dawuda kansa, ta ikon Ruhu Mai Tsarki ya ce, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, Zauna a damana, Sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.’


A shekara ta arbaminya da tamanin bayan fitowar mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar, a shekara ta huɗu ta sarautar Sulemanu, Sarkin Isra'ila, a watan biyu, wato watan Zib, sai Sulemanu ya fara gina Haikalin Ubangiji.


“Ya 'yan'uwa, na iya yi muku magana da amincewa a game da kakanmu Dawuda, cewa ya mutu, an binne shi, kabarinsa kuma yana nan gare mu har ya zuwa yau.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ