Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 2:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Amma muna ganin Yesu, wanda a ɗan lokaci aka sa shi ya gaza mala'iku, an naɗa shi da ɗaukaka da girma, saboda shan wuyarsa ta mutuwa. Wannan kuwa duk ta wurin alherin Allah ne Yesu ya mutu saboda kowa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Sai dai muna ganin Yesu, wanda aka mai da shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku, yanzu kuwa an naɗa shi da ɗaukaka da girma domin yă sha wahalar mutuwa, domin ta wurin alherin Allah yă ɗanɗana mutuwa saboda kowa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 2:9
39 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Suna raira sabuwar waƙa, suna cewa, “Macancanci ne kai ka ɗauki littafin nan, ka ɓamɓare hatimansa, Domin dā an kashe ka, ka kuma fanso wa Allah mutane ta jininka Daga kowace kabila, da kowane harshe, da kowace jama'a, da kowace al'umma,


Shi kansa kuwa shi ne hadayar sulhu saboda gafarta zunubanmu, ba kuwa namu kaɗai ba, har ma na duniya duka.


To, kamar yadda laifin mutum ɗayan nan ya jawo wa dukan mutane hukunci, haka kuma aikin adalci na Mutum ɗayan nan ya zama wa dukan mutane sanadin kuɓuta zuwa rai.


Da yake an ɗaukaka shi a dama ga Allah, ya kuma sami cikar alkawarin nan na baiwar Ruhu Mai Tsarki daga wurin Uba, sai ya zubo da wannan da kuke gani, kuke kuma ji.


“Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.


Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin waɗanda suke a raye, kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.


Shi ya sa da Almasihu zai shigo duniya, sai ya ce, “Hadaya da sadaka kam, ba ka so, Amma kā tanadar mini jiki.


Amma kuwa Allah yana tabbatar mana da ƙaunar da yake yi mana, wato tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu dominmu.


Kashegari Yahaya ya tsinkayo Yesu na nufo shi, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah, wanda zai ɗauke zunubin duniya!


Ni kuwa bayan an ɗaga ni daga ƙasa zan ja dukan mutane gare ni.”


Saboda haka, yana da ikon ceton masu kusatowa ga Allah ta wurinsa, matuƙar ceto, tun da yake kullum a raye yake saboda yi musu addu'a.


Zan sa ƙiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai ƙuje kanka, kai za ka ƙuje diddigensa.”


To gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya ta da shi daga matattu, ya kuma ɗaukaka shi, domin bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.


Kowane babban firist akan sa shi domin ya miƙa sadakoki da hadayu, saboda haka wajibi ne wannan shi ma, ya zamanto yana da abin da zai miƙa.


wanda ya ba da kansa fansa saboda kowa da kowa. An kuwa yi shaidar wannan a daidai lokacinsa.


Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi zunubi saboda mu, domin mu mu sami adalcin Allah ta wurinsa.


Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai ba mu kome tare da shi hannu sake ba?


Amma da lokaci ya yi sosai, sai Allah ya aiko Ɗansa, haifaffen mace, haifaffe kuma a ƙarƙashin Shari'a,


Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, Allahn kakanninmu, shi ya ɗaukaka Baransa Yesu, wanda kuka bashe shi, kuka kuma ƙi shi, a gaban Bilatus, sa'ad da ya ƙudura zai sake shi.


Yanzu fa, Ubangiji kansa zai ba ku alama. Wata budurwa wadda take da ciki, za ta haifi ɗa, za a raɗa masa suna Immanuwel.


Abin da ba shi yiwuwa Shari'a ta yi domin ta kasa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi a cikin jiki, da ya aiko da Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi.


Domin wannan uba yake ƙaunata, domin ina ba da raina in ɗauko shi kuma.


Sai Yahudawa suka ce masa, “To, yanzu kam, mun tabbata kana da iska. Ai, Ibrahim ya mutu, haka ma annabawa, kana kuwa cewa kowa ya kiyaye maganarka ba zai mutu ba har abada.


Hakika, ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba, sai sun ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin Mulkinsa.”


Idanunsa kamar harshen wuta suke, kansa da kambi da yawa, yana kuma da wani suna a rubuce, wanda ba wanda ya sani sai shi.


Kā sa shi ya gaza mala'iku a ɗan lokaci kaɗan, Kā naɗa shi da ɗaukaka da girma, Kā ɗora shi a kan dukkan halittarka.


Amma hakika ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba sai sun ga Mulkin Allah.”


Sai ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba, sai sun ga Mulkin Allah ya bayyana da iko.”


To, don me kuke damuwa a kan tufafi? Ku dubi dai furannin jeji, yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baƙi,


Gidan sarautar Dawuda kamar itacen da aka sare ne, amma kamar yadda rassa sukan toho daga cikin kututture, haka nan za a sami sabon sarki daga zuriyar Dawuda.


Lalle hakika, ina gaya muku, kowa ya kiyaye maganata ba zai mutu ba har abada.”


Kā ƙaunaci aikin adalci, kā ƙi aikin sāɓo. Saboda haka Allah, wato, Allahnka, ya shafe ka Da man farin ciki fiye da tsararrakinka.”


Saboda bangaskiya ce aka ɗauke Anuhu, shi ya sa bai mutu ba, ba a kuwa same shi ba, domin Allah ya ɗauke shi. Tun kafin a ɗauke shi ma, an shaide shi a kan ya faranta wa Allah rai.


muna zuba ido ga Yesu, shi da yake shugaban bangaskiyarmu, da kuma mai kammala ta, wanda domin farin cikin da aka sa a gabansa ya daure wa gicciye, bai mai da shi wani abin kunya ba, a yanzu kuma a zaune yake a dama ga kursiyin Allah.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ