Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 2:4 - Littafi Mai Tsarki

4 sa'an nan kuma Allah ya haɗa shaidarsa, da tasu a kan ceton, ta alamu da abubuwan al'ajabi da mu'ujizai iri iri, da kuma baiwar Ruhu Mai Tsarki dabam dabam da ya rarraba kamar yadda ya nufa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Allah shi ma ya shaida ta wurin alamu, abubuwan banmamaki da mu’ujizai iri-iri, da kuma baye-bayen Ruhu Mai Tsarki da aka rarraba bisa ga nufinsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 2:4
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Bulus da Barnaba suka daɗe a nan ƙwarai, suna wa'azi gabagaɗi bisa ga ikon Ubangiji, shi da ya shaida maganar alherinsa ta yarjin mu'ujizai da abubuwan al'ajabi ta hannunsu.


Ya ƙaddara mu mu zama 'ya'yansa ta wurin Yesu Almasihu, bisa ga nufinsa na alheri,


Su kuwa suka tafi, suka yi ta wa'azi ko'ina, Ubangiji yana taimakonsu, yana kuma tabbatar da maganarsu ta mu'ujizan nan da suke biye da maganar.]


Yesu ya ce masa, “In ba mu'ujizai da abubuwan al'ajabi kuka gani ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.”


Dukan mazaunan duniya ba a bakin kome suke a gare shi ba. Yakan yi yadda ya nufa da rundunar sama da mazaunan duniya, Ba mai hana shi, ba kuma mai ce masa, ‘Me kake yi?’


Amma sa'ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, wato Ruhu na gaskiya, mai fitowa daga wurin Uba, shi ne zai shaida ni.


ya sanasshe mu asirin nufinsa, bisa ga kyakkyawan nufinsa da ya nufa ya cika ta wurin Almasihu.


to, sai ku sani, ku duka, da kuma duk jama'ar Isra'ila, da sunan Yesu Almasihu Banazare, wanda ku kuka gicciye, wanda kuma Allah ya tashi shi daga matattu, albarkacinsa ne mutumin nan yake tsaye a gabanku lafiyayye.


Sai fa sarki Hirudus ya ji labari, domin sunan Yesu ya riga ya shahara, har waɗansu suka ce, “Yahaya Maibaftisma ne aka tasa daga matattu, shi ya sa mu'ujizan nan suke aiki ta wurinsa.”


Mu kuwa shaidu ne ga waɗannan al'amura, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya bai wa masu yi masa biyayya.”


Amma an ba kowannenmu alheri gwargwadon baiwar Almasihu.


Domin waɗanda aka haskaka zukatansu sarai, har suka ɗanɗana baiwar nan ta Basamaniya, suka kuma sami rabo na ruhu mai tsarki,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ