Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.
Ubangiji, wanda yake mulkin Isra'ila, ya kuma fanshe su, Ubangiji Mai Runduna, yake faɗar wannan, “Ni ne farko, da ƙarshe, Allah Makaɗaici, Ba wani Allah sai ni.
Wane ne ya sa wannan ya faru? Wane ne ya ƙudurta labarun tarihi? Ni Ubangiji, ina can tun da farko, Ni kuma Ubangiji Allah, Zan kasance a can har ƙarshe.
Daga Yahaya zuwa ga ikilisiyoyin nan bakwai da suke a ƙasar Asiya. Alheri da salama su tabbata a gare ku daga wanda yake a yanzu, shi ne a dā, shi ne kuma a nan gaba, da kuma Ruhohin nan bakwai da suke a gaban kursiyinsa,
tana cewa, “Rubuta abin da ka gani a littafi, ka aika wa ikilisiyoyin nan bakwai, wato ta Afisa, da ta Simirna, da ta Birgamas, da ta Tayatira, da ta Sardisu, da ta Filadalfiya, da kuma ta Lawudikiya.”
ga Allah makaɗaici Mai Cetonmu ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu, ɗaukaka, da fifiko, da mulki, da iko su tabbata gare shi, tun fil'azal, da yanzu, da kuma har abada abadin. Amin, amin.