Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 13:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Ku yi wa shugabanninku biyayya, ku bi umarnansu, don su ne masu kula da rayukanku, su ne kuma za su yi lissafin aikinsu, don su yi haka da farin ciki, ba da baƙin ciki ba, don in sun yi da baƙin ciki ba zai amfane ku ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Ku yi wa shugabanninku biyayya ku kuma miƙa kanku ga ikonsu. Suna lura da ku kuma za su ba da lissafi a gaban Allah. Saboda haka kada ku sa su yi fushi saboda aikinsu, ku sa su yi farin ciki. In ba haka ba za su iya taimakonku ba ko kaɗan.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 13:17
34 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Dattawan ikkilisiya da suke a riƙe da al'amura sosai, a girmama su ninkin ba ninkin, tun ba ma waɗanda suke fama da yin wa'azi da koyarwa ba.


Ku tuna da shugabanninku na dā, waɗanda suka faɗa muku Maganar Allah. Ku dubi ƙarshensu, ku kuma yi koyi da bangaskiyarsu.


Haka nan ku masu ƙuruciya, ku yi biyayya ga dattawan ikkilisiya. Dukanku ku yi wa kanku ɗamara da tawali'u, kuna bauta wa juna, gama “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana wa masu tawali'u alheri.”


Ku kula da kanku, da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuna kiwon Ikkilisiyar Allah wadda ya sama wa kansa da jininsa.


Amma idan ba za ku ji ba, Raina zai yi kuka a ɓoye saboda girmankanku, Idanuna za su yi kuka ƙwarai, za su zub da hawaye, Domin an kai garken Ubangiji zuwa bauta.


Ina roƙonku ku yi wa irin waɗannan mutane biyayya, har ma ga duk waɗanda suke abokan aikinmu da wahalarmu.


Saboda haka, ya ƙaunatattuna, kamar yadda a kullum kuke biyayya, haka kuma yanzu, ku yi ta yin aikin ceton nan naku da halin bangirma tare da matsananciyar kula, ba ma sai ina nan kawai ba, har ma fiye da haka in ba na nan.


Musa ya koma wurin Ubangiji, ya ce, “Kaito, mutanen nan sun aikata zunubi mai girma, sun yi wa kansu gunkin zinariya.


Don haka sai ku karɓe shi da matuƙar farin ciki saboda Ubangiji, ku kuma girmama irin waɗannan mutane,


Don haka kowannenmu zai faɗi abin da shi da kansa ya yi, a gaban Allah.


In wani ya ƙi bin abin da muka faɗa a wasiƙar nan, sai fa ku lura da shi, kada ma ku yi cuɗanya da shi, don yă kunyata.


Ku gai da dukan shugabanninku, da kuma dukan tsarkaka. Waɗanda suke daga ƙasar Italiya suna gaishe ku.


Ya Urushalima, na sa matsara a garukanki Ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana. Za su tuna wa Ubangiji da alkawaransa, Ba kuwa za su bari ya manta ba!


Saboda haka ya 'yan'uwana, ƙaunatattuna, waɗanda nake bege, ku da kuke abin farin cikina da abin taƙamata kuma, ku dage ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna.


Domin da yawa waɗanda na sha gaya muku, yanzu kuma nake gaya muku, har da hawaye, suna bin Yesu, in ji su, amma su magabtan gicciyen Almasihu ne.


Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah, ku yi tsayayya da Iblis, lalle kuwa zai guje muku.


a kullum kuwa a kowace addu'a da nake muku duka, da farin ciki nake yi.


Sai ya kira shi ya ce masa, ‘Labarin me nake ji naka? Kawo lissafin wakilcinka, don ba sauran ka zama wakilina.’


Ban kasa kunne ga malamaina ba. Ban mai da hankalina gare su ba.


Amma mutane suka ƙi jin abin da Sama'ila ya faɗa musu, sai suka ce, “Duk da haka dai, muna so sarki ya sarauce mu,


Mala'ikan Ubangiji ya ce mata, “Koma wurin uwargijiyarki, ki yi mata ladabi.”


kuna riƙe da maganar rai kankan, har a ranar bayyanar Almasihu in yi taƙama, cewa himmata da famana ba a banza suke ba.


“Ɗan mutum, ka yi magana da mutanenka, ka faɗa musu cewa, ‘Idan na zare takobi a kan wata ƙasa, idan mutanen ƙasar suka ɗauki wani mutum daga cikinsu, suka sa shi ya zama ɗan tsaronsu,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ