Ibraniyawa 13:15 - Littafi Mai Tsarki15 To, a koyaushe, sai mu yi ta yabon Allah ta wurinsa, sadakar da muke miƙawa ke nan, wato mu yabe shi, muna ta ɗaukaka sunansa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202015 Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai firistoci suka tsaya a matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a nasu matsayi riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji, gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce har abada. A duk lokacin da Dawuda zai yabi Ubangiji tare da su, sai firistoci waɗanda suke daura da su su busa ƙaho, sa'an nan sai dukan Isra'ilawa su miƙe tsaye.
za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa'ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa, “ ‘Ku yi godiya ga Ubangiji Mai Runduna, Gama Ubangiji nagari ne, Gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce.’ “Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.”