Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 13:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Domin ba mu da wani dawwamammen birni a nan, birnin nan mai zuwa muke nema.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Gama a nan ba mu da dawwammamen birni, sai dai muna zuba ido a kan birnin nan mai zuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 13:14
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Mu kuwa 'yan Mulkin Sama ne, daga can ne kuma muke ɗokin zuwan Mai Ceto, Ubangiji Yesu Almasihu,


Amma ku kun iso Ɗutsen Sihiyona ne, da birnin Allah Rayayye, Urushalima ta Sama, wurin dubban mala'iku.


Wato ashe, ku ba baƙi ba ne kuma, ko kuwa bāre, ai, ku abokan 'yanci ne na tsarkaka, iyalin Allah kuma,


Don wannan 'yar wahalar tamu, mai saurin wucewa ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci.


Abin da nake nufi 'yan'uwa, lokacin da aka ƙayyade ya ƙure. A nan gaba masu mata su zauna kamar ba su da su,


Ku tashi, ku tafi, Gama nan ba wurin hutawa ba ne, Saboda ƙazantarku wadda take kawo muguwar hallaka.


Ƙarshen dukan abubuwa ya gabato. Saboda haka, sai ku kanku, ku natsu, domin ku yi addu'a.


wato, har yanzu dai akwai sauran wani hutun Asabar ga jama'ar Allah,


Ai, ba ga mala'iku ba ne Allah ya sa mulkin duniyar da za a yi, wanda muke zance.


Amma Almasihu ya riga ya zo, yana babban firist na kyawawan abubuwan da suke akwai. Masujadar da yake hidima a ciki mafi ɗaukaka ce, mafi kammala kuwa (wadda ba yin mutum ba ce, wato, ba ta wannan halittacciyar duniya ba ce).


domin kun ji tausayin ɗaurarru, kun kuma yarda da daɗin rai da wason da aka yi muku, tun da yake kun sakankance kuna da mallaka mafi kyau, mai tabbata kuwa.


To, wannan cewa, “Har wa yau dai sau ɗaya tak,” ya nuna kawar da abubuwan da aka girgiza, wato abubuwan da aka halitta, don abubuwan da ba sa girgizuwa su wanzu.


Duk wanda ya ci nasara, zan mai da shi ginshiƙi a Haikalin Allahna. Ba zai ƙara fita daga ciki ba, zan kuma rubuta sunan Allahna a jikinsa, da sunan Birnin Allahna, wato, Sabuwar Urushalima, mai saukowa daga wurin Allahna daga Sama, da kuma nawa sabon suna.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ