Yau za ku sani Ubangiji Allahnku yake muku ja gaba sa'ad da kuke hayewa. Shi wuta ne mai cinyewa, zai hallaka su, ya rinjayar muku su, domin ku kore su, ku hallaka su nan da nan kamar yadda Ubangiji ya alkawarta muku.
“Ina dubawa sai na ga an ajiye gadajen sarauta, Sai wani wanda yake Tun Fil Azal ya zauna kursiyinsa. Rigarsa fara fat kamar dusar ƙanƙara, Gashin kansa kamar ulu ne tsantsa, Kursiyinsa harshen wuta ne, Ƙafafun kursiyin masu kamar karusa, wuta ne.
Jama'ar Sihiyona cike da zunubi suke, suna ta rawar jiki don tsoro. Suka ce, “Hukuncin Allah kamar wuta ce mai ci har abada. Akwai wani daga cikinmu da zai iya tsira daga irin wannan wuta?”
Da yake muna tsoron Ubangiji, shi ya sa muke ƙoƙarin rinjayar mutane. Yadda muke kuwa, ai, sananne ne ga Allah, muna fata ku ma haka abin yake a lamirinku.
yă kuma ba ku hutu har da mu ma, ku da ake ƙuntata wa ɗin, a ranar bayyanar Ubangiji Yesu daga Sama tare da manyan mala'ikunsa, a cikin wuta mai ruruwa,
Ta maganar Allah ne kuma sama da ƙasa da suke a nan a yanzu, aka tanada su ga wuta, ana ajiye su, har ya zuwa ranar nan da za a yi wa marasa bin Allah shari'a, a hallaka su.