Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 12:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Ai, kowane irin horo, a lokacin shansa, abu ne mai baƙin ciki, ba na farin ciki ba. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Babu horon da yake da daɗi a lokacin da ake yinsa, sai dai zafi. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 12:11
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Don wannan 'yar wahalar tamu, mai saurin wucewa ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci.


A kan wannan ne kuke da matuƙar farin ciki, ko da yake da ɗan lokaci kwa yi baƙin ciki ta dalilin gwaje-gwaje iri iri.


Su kam, sun hore mu a ɗan lokaci kaɗan don ganin damarsu, amma shi, don amfanin kanmu ne yake horonmu, domin mu zama abokan tarayya a cikin tsarkinsa.


Ya hukunta ni da hukunci mai tsanani, Amma bai kashe ni ba.


Gama kowa zai yi abin da yake daidai, za a sami salama da zaman lafiya har abada.


Ka yi wa 'ya'yanka tarbiyya tun suna ƙanana yadda za su iya koyo. Idan ba ka yi haka ba, ka taimaka wajen lalacewarsu ke nan.


Waɗanda suke ƙaunar dokarka sun sami cikakken zaman lafiya, Ba wani abin da zai sa su fāɗi.


Idan ka yi abin da ba daidai ba, za ka sha hukunci sosai, za ka mutu idan ka ƙi yarda da tsautawa.


Amma abinci mai tauri, ai, na manya ne, wato waɗanda hankalinsu ya horu yau da kullum, su rarrabe nagarta da mugunta.


Ai, Mulkin Allah ba ga al'amarin ci da sha yake ba, sai dai ga adalci, da salama da farin ciki ta wurin Ruhu Mai Tsarki.


To, sai in hukunta su saboda zunubansu, Zan bulale su saboda laifofinsu.


Jarabar zina take a gare su, ba sa ƙoshi da yin zunubi. Suna yaudarar marasa kintsuwa. Sun ƙware da ƙwaɗayi. La'anannun iri!


Ubangiji zai hukunta Masarawa, amma zai warkar da su. Za su juyo gare shi, shi kuma zai ji addu'o'insu ya warkar da su.


Saura kuwa, sai sakamakon nan na aikin adalci, da aka tanadar mini, wanda Ubangiji, mahukunci mai adalci, zai ba ni a ranar nan, ba kuwa ni kaɗai ba, har da duk waɗanda suke ɗokin ganin bayyanarsa.


Abin ya ɓata wa Ibrahim zuciya ƙwarai sabili da ɗansa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ