Ibraniyawa 11:7 - Littafi Mai Tsarki7 Ta wurin bangaskiya Nuhu, da Allah ya yi masa gargaɗi a kan al'amuran da ba a gani ba a lokacin, yana tsoron Allah, ya sassaƙa jirgi, don ceton iyalin gidansa, ta wurin bangaskiya kuma ya tabbatar wa duniya laifinta, har ya zama magājin adalcin Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Ta wurin bangaskiya Nuhu, sa’ad da aka yi masa gargaɗi a kan abubuwan da ba a gani ba tukuna, a cikin tsoro mai tsarki ya sassaƙa jirgi don ceton iyalinsa. Ta wurin bangaskiyarsa ya hukunta duniya ya kuma zama magājin adalcin da ake samu ta wurin bangaskiya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |