Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 11:38 - Littafi Mai Tsarki

38 Su kam, duniya ba ta ma cancanci su zama a cikinta ba. Sun yi yawo a jazza da a kan duwatsu, suna kwana a cikin kogwanni da ramummuka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

38 duniya ba tă ma cancanci su zauna a cikinta ba. Suka yi ta yawo a cikin hamada da a kan duwatsu, da cikin kogwanni da kuma cikin ramummuka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 11:38
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A lokacin da Yezebel ta karkashe annabawan Ubangiji, Obadiya ya kwashe annabawa ɗari ya raba su hamsin hamsin ya ɓoye su a kogo, ya ciyar da su, ya shayar da su.


A can ya shiga wani kogo domin ya kwana. Ba labari sai Ubangiji ya yi magana da shi, ya ce masa, “Me kake yi a nan, Iliya?”


Dawuda ya bar Gat, ya tsere zuwa kogon Adullam. Da 'yan'uwansa da mutanen gidan ubansa, suka ji labari, suka tafi can wurinsa.


Adalin mutum yakan mutu, amma ba wanda ya kula. An kwashe mutanen kirki ba kuwa wanda ya kula, an tsame adali daga cikin bala'i.


Ashe, ba ka ji ba? Na kasa annabawan Ubangiji biyu, na ɓoye su a kogo hamsin hamsin, sa'ad da Yezebel ta kashe annabawan Ubangiji, na ciyar da su, na kuma shayar da su.


“Ka tashi daga nan ka nufi wajen gabas, ka ɓuya a rafin Kerit, a gabashin Urdun.


Zifawa suka zo wurin Saul a Gibeya suka ce, “Ba ga Dawuda yana ɓuya a kan tudun Hakila wanda yake gaban Yeshimon ba?”


Ku lura sosai da dukan wuraren da yake ɓuya, sa'an nan ku komo mini da tabbataccen labari. Sa'an nan zan tafi tare da ku. Idan yana ƙasar, zan neme shi ko'ina a ƙasar Yahuza.”


Sai Zifawa suka haura zuwa wurin Saul a Gibeya, suka ce masa, “Dawuda ya ɓuya a ƙasarmu cikin Horesh a kan tudun Hakila da yake kudu da jejin Yahuza.


Dawuda kuwa ya ji tsoro, gama Saul ya fito don ya farauci ransa. Sa'ad da yake cikin jejin Zif, a Horesh, sai Jonatan ɗan Saul, ya zo wurinsa, ya tabbatar masa da kiyayyewar Allah.


Madayanawa kuwa sun fi Isra'ilawa ƙarfi, saboda haka Isra'ilawa suka yi ta ɓuya a kogon dutse, da waɗansu wuraren ɓuya a tsaunuka.


Rijiyar da Isma'ilu ya zuba dukan gawawwakin mutanen da ya kashe mai zurfi ce, sarki Asa ne ya haƙa saboda tsoron Ba'asha Sarkin Isra'ila. Isma'ilu ɗan Netaniya kuwa ya cika ta da gawawwakin mutanen da ya kashe.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ