Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 11:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Ta wurin bangaskiya ya bar Masar, bai ji tsoron fushin sarki ba, ya kuwa jure saboda yana ganin wannan da ba ya ganuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 Ta wurin bangaskiya ya bar Masar, ba tare da jin tsoron fushin sarki ba; ya kuwa jure domin ya ga wannan wanda ba a iya gani.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 11:27
27 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Waɗannan duka sun mutu cikin bangaskiyarsu, ba su kuwa sami abubuwan da aka yi musu alkawari ba, amma da suka tsinkato su, sai suka yi ta murna da ganinsu, suna kuma yarda su baƙi ne, bare kuma a duniya.


Domin ba abubuwan da ido yake gani muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa, gama abubuwan da ake gani, masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.


To, bangaskiya kuwa ita ce haƙƙaƙewar abubuwan da ake bege, a kai, ita ce kuma tabbatawar abubuwan da ba a gani ba.


Ga shi, mukan yaba wa waɗanda suka jure. Kun dai ji irin jimirin da Ayuba ya yi, kun kuma ga irin ƙarshen da Ubangiji ya yi masa, yadda Ubangiji yake mai yawan tausayi, mai jinƙai kuma.


Sa'an nan dukan fādawanka za su zo wurina su fāɗi a gabana suna cewa, ‘Ka fita, kai da dukan jama'arka!’ Sa'an nan zan fita.” Daga nan sai Musa ya fita daga gaban Fir'auna a husace.


Ubangiji kuwa ya faɗa wa Musa a Madayana, ya koma Masar, gama dukan waɗanda suke neman ransa sun rasu.


Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa. Ko da yake ba kwa ganinsa a yanzu, duk da haka kuna gaskatawa da shi, kuna farin ciki matuƙa, wanda ya fi gaban ambato,


Amma dai ku tuna, a shekarun baya, bayan da aka haskaka zukatanku, kun jure tsananin fama da shan wuya,


Girma da ɗaukaka su tabbata ga Sarkin zamanai, marar mutuwa, marar ganuwa, Allah Makaɗaici, har abada abadin. Amin, amin.


Ƙauna tana sa daurewa a cikin kowane hali, da bangaskiya a cikin kowane hali, haka kuma sa zuciya a cikin kowane hali, da jimiri a cikin kowane hali.


Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu.


Ga yadda za ku ci shi, da ɗamara a gindinku, da takalma a ƙafafunku, da sanda a hannunku, da gaggawa kuma za ku ci shi. Idin Ƙetarewa ne ga Ubangiji.


Ta haka Ibrahim, bayan da ya jure da haƙuri, ya karɓi cikar alkawarin.


Shi ne kaɗai marar mutuwa, yake kuma zaune a cikin hasken da ba ya kusatuwa. Shi kuwa ba mutumin da ya taɓa ganinsa, ko kuwa zai iya ganinsa. Girma da madawwamin mulki su tabbata a gare shi. Amin, amin.


Dawuda kuma ya yi faɗi a game da shi ya ce, “ ‘Kullum hankalina yana kan Ubangiji, Yana damana, domin kada in jijjigu.


Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe zai cetu.”


Su kam, ba su da tushe, rashin ƙarƙo gare su, har in wani ƙunci ko tsanani ya faru domin wannan Magana, nan da nan sai su yi tuntuɓe.


Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu.


A kullum ina jin Ubangiji yana tare da ni, Yana nan kusa, ba abin da zai girgiza ni.


Isra'ilawa suka yi na'am da shi, suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna.


Shi ne surar Allah marar ganuwa, magāji ne tun ba a halicci kome ba,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ